7:1A. L̃. M̃. Ṣ̃.
7:2Littãfi ne aka saukar zuwa gare ka, kada wani ƙunci ya kasance a cikin ƙirjinka daga gare shi, dõmin ka yi gargaɗi da shi. Kuma tunãtarwa ne ga mũminai.
7:3Ku bi abin da aka saukar zuwa gare ku daga Ubangijinku, kuma kada ku dinga bin wasu majiɓinta baicinSa. Kaɗan ƙwarai kuke tunãwa.
7:4Kuma da yawa wata alƙarya Muka halaka ta, sai azãbarMu ta jẽ mata da dare kõ kuwa sunã mãsu ƙailũla.
7:5Sa'an nan bãbu abin da yake da'awarsu, a lõkacin da azãbarMu ta jẽ musu, fãce suka ce: "Lalle ne mũ muka kasance mãsu zãlunci,"
7:6Sa'an nan lalle ne Munã tambayar waɗanda aka aika zuwa gare su, kuma lalle Munã tambayar Manzannin.
7:7Sa'an nan haƙĩƙa Munã bã su lãbãri da ilmi kuma ba Mu kasance mãsu fakowa ba.
7:8Kuma awo a rãnar nan ne gaskiya. To, wanda sikẽlansasuka yi nauyi, to, waɗannan sũ ne mãsu cin nasara.
7:9Kuma wanda sikẽlansa suka yi sauƙi, to, waɗannan ne waɗanda suka yi hasarar rayukansu, sabõda abin da suka kasance, da ãyõyinMu, sunã yi na zãlunci.
7:10Kuma lalle ne haƙĩƙa, Mun sarautar da ku, a cikin ƙasa, kuma Mun sanya muku abũbuwan rãyuwa, a cikinta; kaɗan ƙwarai kuke gõdẽwa.
7:11Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun halittã ku sa'an nan kuma Mun sũrantã ku, sa'an nan kumaMun ce wa malã'iku: "Ku yi sujada ga Ãdam." Sai suka yi sujada fãce Iblĩs, bai kasance daga mãsuyin sujadar ba.