Ana lodawa...
2:1A. L̃. M̃.
2:2Wãncan ne Littãfi, bãbu shakka a cikinsa, shiriya ne ga mãsu taƙawa.
2:3Waɗanda suke yin ĩmãni game da gaibi, kuma suna tsayar da salla, kuma daga abin da Muka azurta su suna ciyarwa.
2:4Kuma waɗanda suke yin ĩmãni da abin da aka saukar zuwa gare ka, da abin da aka saukar daga gabãninka, kuma game da Lãhira suna yin yaƙĩni.
2:5Waɗannan suna kan shiriya, daga Ubangjinsu, kuma waɗannan su ne mãsu cin nasara.