15:91Waɗanda suka sanya Alƙur'ãni tãtsuniyõyi.
15:92To, rantsuwa da Ubangijinka! Haƙĩƙa, Munã tambayarsugabã ɗaya.
15:93Daga abin da suka kasance sunã aikatãwa.
15:94Sai ka tsage gaskiya game da abin da ake umurnin ka kuma ka kau da kai daga masu shirki.
15:95Lalle ne Mũ Mun isar maka daga mãsu izgili.
15:96Waɗanda suke sanyãwar wani abin bautãwa na dabam tare da Allah, sa'an nan da sannu zã su sani.
15:97Kuma lalle ne haƙĩƙa Munã sanin cẽwa lalle kai, ƙirjinka yanã yin ƙunci game da abin da suke faɗã (na izgili).
15:98Sabõda haka ka yi tasbĩhi game da gõde wa Ubangijinka, kuma ka kasance daga mãsu sujada.
15:99Kuma ka bauta wa Ubangijinka, har mutuwa ta zo maka.
16:1Al'amarin Allah yã zo, sabõda haka kada ku nẽmi hanzartãwarsa. Tsarkin Allah ya tabbata, kuma Ya ɗaukaka daga abin da suke yi na shirka.
16:2Yanã sassaukar da malã'iku da Rũhi daga umurninSaa kan wanda Yake so daga bãyinSa, cẽwa ku yi gargaɗi cẽwa: Lalle ne shĩ, bãbu abin bautãwa fãce Ni, sabõda haka ku bĩ Ni da taƙawa.
16:3Ya halicci sammai da ƙasa da gaskiya. Ya ɗaukaka daga abin da suke yi na shirka.
16:4Ya halicci mutum daga maniyyi, sai gã shi yanã mai husũma bayyananniya.
16:5Da dabbõbin ni'ima, Ya halicce su dõminku. A cikinsu akwai abin yin ɗumi da waɗansu amfãnõni, kuma daga gare su kuke ci.
16:6Kuma kunã da kyau a cikinsu a lõkacin da suke kõmõwa daga kĩwo da maraice da lõkacin da suke sakuwã.