19:96Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyuka na ƙwarai, Mai rahama zai sanya musu so.
19:97Sa'an nan Ibin sani kawai Mun sauƙaƙar da shi (Alƙur'ãni) a harshenka, dõmin ka yi bushãra da shi ga mãsu aiki da taƙawa kuma ka yi gargaɗi da shi ga mutãne mãsu tsananin husũma.
19:98Kuma da yawa Muka halakar da mutãnen ƙarnõni a gabãninsu. Shin kanã jin mõtsin wani guda daga gare su, kõ kuwa kanã jin wata ɗuriya tãsu?
20:1¦.H.
20:2Ba Mu saukar da Alƙur'ãni a gare ka dõmin ka wahala ba.
20:3Fãce dõmin tunãtarwa ga wanda ke tsõron Allah.
20:4(An saukar da shi) saukarwa daga wanda Ya halitta ƙasa da sammai maɗaukaka.
20:5Mai rahama, Ya daidaita a kan Al'arshi.
20:6Abin da yake a cikin sammai nãSa ne, da abin da yake a cikin ƙasa da abin da yake a tsakãninsu da abin da ke ƙarƙashin turɓãya.
20:7Kuma idan ka bayyana da magana, to, lalle Shi, Yanã sanin asĩri da mafi bõyuwa.
20:8Allah bãbu abin bautãwa fãce Shi. Yanã da sunãye mafiya kyau.
20:9Kuma shin, lãbarin Mũsã yãje maka?
20:10A lõkacin da ya ga wata wuta, sai ya ce wa iyãlinsa, "Ku dãkata. Lalle ne nĩ, na tsinkãyi wata wuta tsammãnĩna in zo mukuda makãmashi daga gare ta, kõ kuwa in sãmi wata shiriya a kan wutar."
20:11Sa'an nan a lõkacin da ya je mata, aka kira shi, "Ya Mũsã!"
20:12"Lalle ne, Nĩ ne Ubangijnka, sai ka ɗẽbe takalmanka Lalle ne kanã a rãfin nan abin tsarkakẽwa, ¦uwa."