23:1Lalle ne, Mũminai sun sãmi babban rabõ.
23:2Waɗanda suke a cikin sallarsu mãsu tawãli'u ne.
23:3Kuma waɗanda suke, sũdaga barin yasassar magana, mãsu kau da kai ne.
23:4Kuma waɗanda suke ga zakka mãsu aikatãwa ne.
23:5Kuma waɗanda suke ga farjõjinsu mãsu tsarẽwa ne.
23:6Fãce a kan mãtan aurensu, kõ kuwa abin da hannayen dãmansu suka mallaka to lalle sũ bã waɗanda ake zargi, ba, ne.
23:7Sabõda haka wanda ya nẽmi abin da ke bãyan wancan, to, waɗancan sũ ne mãsu ƙẽtarẽwar haddi.
23:8Kuma waɗanda suke, sũga amãnõninsu da alkawarinsu mãsu tsarẽwa ne.
23:9Kuma da waɗanda suke, sũ a kan sallõlinsu sunã tsarẽwa.
23:10Waɗannan, sũ ne magãda.
23:11Waɗanda suke gãdõn (Aljannar) Firdausi, su a cikinta madawwama ne.
23:12Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun halitta mutum daga wani tsantsa daga lãka.
23:13Sa'an nan kuma Muka sanya shi, ɗigon maniyyi a cikin matabbata natsattsiya.
23:14Sa'an nan kuma Muka halitta shi gudan jini, sa'an nan Muka halitta gudan jinin tsõka, sa'an nan Muka halitta tsõkar ta zama ƙasũsuwa, sa'an nan Muka tufãtar da ƙasũsuwan da wani nãma sa'an nan kuma Muka ƙãga shi wata halitta dabam. Sabõda haka albarkun Allah sun bayyana, Shi ne Mafi kyaun mãsu halittawa.
23:15Sa'an nan kuma ku, bãyan wannan, lalle ne masu mutuwa ne.
23:16Sa'an nan kuma lalle ne kũ a Rãnar ¡iyãma, za a iãyar da ku,
23:17Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun halitta, a samanku, hanyõyi bakwai, kuma ba Mu kasance, daga barin halittar, Mãsu shagala ba.