27:89Wanda ya zo da kyakkyawan aiki guda, to, yanã da mafi alhẽri daga gare shi. Kuma sũ daga wata firgita, a yinin nan, amintattu ne.
27:90Kuma wanda ya zo da mugun aiki, to, an kife fuskõkinsu a cikin wuta. Ko zã a sãka muku fãce da abin da kuka kasance kũnã aikatãwa?
27:91(Ka ce): "An umurce ni, in bauta wa Ubangijin wannan Gari, Wanda Ya mayar da shi Hurumi, kuma Yanã da dukan kõme. Kuma an umurce ni da in kasance daga mãsu sallamãwa."
27:92"Kuma inã karanta Alƙur'ãni." To, wanda ya shiryu, yã shiryu ne dõmin kansa kawai. Kuma wanda ya ɓãce, to, ka ce: "Ni daga mãsu gargaɗi kawai nake."
27:93Kuma ka ce: "Gõdiya ta tabbata ga Allah. Zai nũna muku ãyõyinSa, har ku sansu." Kuma Ubangijinka bai zama Mai shagala daga barin abin da kuke aikatãwa ba.
28:1¦. S̃. M̃.
28:2Waɗancan ãyõyin Littãfi ne bayyananne.
28:3Munã karantãwa a kanka daga lãbarin Mũsã da Fir'auna da gaskiya dõmin mutãne waɗanda suke yin ĩmãni.
28:4Lalle ne Fir'auna ya ɗaukaka a cikin ƙasa, kuma ya sanya mutãnenta ƙungiya-ƙungiya, yanã raunanar da wata jama'a daga gare su; yanã yanyanka ɗiyansu maza kuma yanã rãyar da mãtan. Lalle shĩ ya kasance daga mãsu ɓarna.
28:5Kuma Munã nufin Mu yi falala ga waɗanda aka raunanar a cikin ƙasar, kuma Mu sanya su shugabanni, kuma Mu sanya su magãda.