29:64Kuma wannan rãyuwa ta dũniya ba ta zamo ba, fãce abar shagala da wãsã kuma lalle Lãhira tabbas, ita ce rãyuwa, dã sun kasance sunã sani.
29:65To, a lõkacin da suka shiga cikin jirgin ruwa, sun kirãyi Allah sunã mãsu tsarkake addini a gare shi, to, a lõkacin da Ya tsĩrar da su zuwa ga tudun ƙasã, sai gã su sunã shirki.
29:66Dõmin su kãfirce wa abin da Muka bã su kuma dõmin su ji dãɗi sa'an nan kuma zã su sani.
29:67Shin, ba su ga cẽwa, lalle Mun sanya Hurumi amintacce ba alhãli kuwa anã fisge mutãne a gẽfensu? Shin, da ɓãtaccen abu suke ĩmãni kuma da ni'imarAllah suka kãfirta?
29:68Kuma wãne ne ya fi zãlunci bisa ga wanda ya ƙirƙira ƙarya ya jingina ta ga Allah, kõ kuma ya ƙaryata gaskiya a lõkacin da ta je masa? Ashe a cikin Jahannama bãbu mazauna ga kãfirai?
29:69Kuma wadannan da suka yi ƙõƙari ga nẽman yardarMu, lalle Munã shiryar da su ga hanyõyinMu, kuma lalle Allah, tabbas, Yanã tãre da mãsu kyautatãwa (ga addĩninsu).
30:1A. L̃. M̃.
30:2An rinjãyi Rũmawa.
30:3A cikin mafi kusantar ƙasarsu, kuma sũ, a bãyan rinjãyarsu, zã sn rinjãya.
30:4A cikin'yan shẽkaru. Al'amari na Allah ne a gabãnin kõme da bãyansa, kuma a rãnar nan mũminai zã su yi farin ciki.
30:5Da taimakon Allah Yanã taimakon wanda Yake so. Kuma Shĩ ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai.