35:45Kuma dã Allah Yanã kãma mutãne sabõda abin da suka aikata, dã bai bar wata dabba ba a kanta (kasã). Amma Yanã jinkirta musu zuwa ga ajalin da aka ambatã. Sa'an nan idan ajalinsu ya zo, to, lalle Allah yã kasance Mai gani ga bãyinSa.
36:1Y. S̃.
36:2Inã rantsuwa da Al-ƙur'ãni Mai hikima.
36:3Lalle kai, haƙĩƙa kanã cikinManzanni.
36:4A kan hanya madaidaiciya.
36:5(Allah Ya saukar da Al-kur'ãni) saukarwar Mabuwãyi, Mai jin ƙai.
36:6Dõmin ka yi gargaɗi ga waɗansu mutãne da ba a yi gargaɗi ga ubanninsu ba, sabõda haka sũmasu rafkana ne.
36:7Lalle, haƙĩƙa, kalma tã wajaba a kan mafi yawansu, dõmin sũ, bã zã su yi ĩmãni ba.
36:8Lalle Mũ, Mun sanya ƙuƙumma a cikin wuyõyinsu, sa'an nan sũ (ƙuƙumman sun kai) har zuwa ga haɓõɓinsu, sabõda haka, sũ banƙararru ne.
36:9Kuma Muka sanya wata tõshiya a gaba gare su, da wata tõshiya a bãyansu, sabõda haka Muka rufe su, sai suka zama bã su gani.
36:10Kuma daidai yake a gare su, shin, ka yi musu gargaɗi kõ ba ka yi musu gargaɗi ba, sũ bã zã su yi ĩmãni ba.
36:11Kanã yin gargaɗi kawai ga wanda ya bi Alƙur'ãni ne, kuma ya ji tsõron mai rahama a fake. To, ka yi masa bushãra da gãfara da wani sakamako na karimci.
36:12Lalle Mũ, Mũ ne ke rãyar da matattu kuma Mu rubũta abin da suka gabãtar, da gurãbunsu, kuma kõwane abu Mun ƙididdige shi, a cikin babban Littãfi Mabayyani.