38:1Ṣ̃, Inã rantsuwa da Al-ƙur'ãni mai hukunce-hukunce.
38:2Ã'a, waɗanda suka kãfirta sunã cikin girman kai (ga rikon al'ãdunsu) da sãɓãni (tsakãnin jũnansu).
38:3Da yawa Muka halakar da wani ƙarni, a gabãninsu, suka yi kira (nẽman cẽto), bãbu lõkacin kuɓucewa.
38:4Kuma suka yi mãmãki dõmin Mai gargaɗi, daga cikinsu, ya je musu. Kuma kãfirai sukace, "Wannan mai sihiri ne, maƙaryaci."
38:5"Shin, yã sanya gumãka duka su zama abin bautawa guda? Lalle wannan, haƙĩƙa, abu ne mai ban mãmaki!"
38:6Shũgabanni daga cikinsu, suka tafi (suka ce),"Ku yi tafiyarku, ku yi haƙuri a kan abũbuwan bautawarku. Lalle wannan, haƙiƙa, wani abu ne ake nufi!"
38:7"Ba mu taɓa ji ba, game da wannan a cikin addinin ƙarshe. Wannan bai zama ba fãce ƙiren ƙarya."
38:8"Shin, an saukar da Alƙur'ãni ne a kansa, a tsakãninmu (mũ kuma ba mu gani ba)?" Ã'a, su dai sunã cikin shakka daga hukunciNa Ã'a, ba su i da ɗanɗanar azãba ba.
38:9Ko kuma a wurinsu ne ake ajiye taskõkin rahamar Ubangijinka, Mabuwãyi, Mai yawan kyauta?
38:10Kõ kuma sũ ne da mallakar sammai da ƙasã da abin da ke a tsakãninsu? To sai su hau a cikin sammai (dõmin, su hana saukar Alƙur'ãni ga Muhammadu).
38:11Rundunõni ne abin da ke can, rusassu, na ƙungiyõyinsu.
38:12Mutãnen Nũhu sun ƙaryata, a gabãninsu, da Ãdãwa da Fir'auna mai turãkun (da suka kafe mulkinsa).
38:13Da Samũdãwa da mutãnen Luɗu da ma'abũta ƙunci, waɗancan ne ƙungiyõyin.
38:14Bãbu kõwa a cikinsu fãce ya ƙaryata Manzanni, sabõda haka azãbãTa ta wajaba.
38:15Kuma waɗannan bã su jiran kõme fãce tsãwã guda, wadda bã ta da hani.
38:16Kuma suka ce: "Ya Ubangijinmu! Ka gaggauta mana da rabonmu, a gabãnin rãnar bincike."