41:1Ḥ. M̃.
41:2Saukarwa (da Alƙur' ãni) dãga Mai rahama ne, Mai jin ƙai.
41:3Littãfi ne, an bayyana ãyõyinsa daki-daki, yanã abin karantãwa na Lãrabci, dõmin mutãnen dake sani
41:4Yanã mai bãyar da bushãra kuma mai gargaɗi. Sai mafi yawansu suka bijire. Sabõda haka sũ, bã su saurãrãwa.
41:5Kuma suka ce: "Zukatanmu nã a cikin kwasfa daga abin da kake Kiran mu zuwa gare shi, kuma a cikin kunnuwanmu akwai wani nauyi, kuma daga tsakaninmu da tsakaninka akwai wani shãmaki. sahõda haka ka yi aiki, lalle mũ mãsu aiki ne."
41:6Ka ce: "Nĩ mutum kawai ne kamarku, ãnã yin wahayi zuwa gare ni cẽwa abin bautãwarku, abin bautãwa guda ne. Sai ku daidaitu zuwa gare Shi, kuma ku nẽmi gafararSa." Kuma bone ya tabbata ga mãsu yin shirki.
41:7Waɗanda bã su bãyar da zakka, kuma sũ a game da Lãhira su kafirai ne.
41:8Lalle wɗdanda suka yi ĩmãni, Kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, sunã da wani sakamako wanda bai yankẽwa.
41:9Ka ce: "Ashe lalle kũ, haƙĩƙa, kunã kafurta a game da wanda Ya halitta kasã a cikin kwanuka biyu, kuma kunã sanya Masa kĩshiyõyi? Wancan fa, shĩ ne Ubangijin halittu."
41:10Kuma Ya sanya, a cikinta, dũwatsu kafaffu daga samanta, kuma Ya sanya albarka a cikinta, kuma Ya ƙaddara abũbuwan cinta a cikinta a cikin kwanuka huɗu mãsu daidaita, dõmin matambaya.
41:11Sa'an nan Ya daidaita zuwa ga sama alhãli kuwa ita (a lõkacin) hayãƙi ce, sai Ya ce mata, ita da ƙasã "Ku zo, bisa ga yarda kõ a kan tĩlas." Suka ce: "Mun zo, munã mãsu ɗã'ã. "