47:1Waɗanda suka kãfirta kuma suka kange mutãne daga tafarkin Allah, (Allah) Ya ɓatar da ayyukansu.
47:2Kuma waɗanda suka yi ĩmani, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, kuma suka yi ĩmani da abinda aka sassaukar ga Muhammadu, alhãli kuwa shĩ ne gaskiya daga Ubangijinsu, (Allah) Yã karkare musu miyãgun ayyukansu, kuma Yã kyautata hãlãyensu.
47:3Wannan kuwa sabõda lalle, waɗanda suka kãfirta sun bi ƙarya, kumar lalle waɗanda suka yi ĩmãni, sun bi gaskiya daga Ubangijinsu. Kamar wannan ne Allah Yake bayyana wa mutãne misãlansu.
47:4Sabõda haka idan kun haɗu da waɗanda suka kãfirta, sai ku yi ta dũkan wuyõyinsu har a lõkacin da suka yawaita musu kisa, to, ku tsananta ɗaurinsu sa'an nan imma karimci a bãyan' haka kõ biyan fansa, har yãƙi ya saukar da kayansa mãsu nauyi. Wancan, dã Allah nã so da Ya ci nasara a kansu (ba tare da yaƙin ba) kuma amma (ya wajabta jihadi) dõmin Ya jarraba sãshenku da sãshe. Kuma waɗanda zaka kashe a cikin tafarkin Allah, to, bã ai ɓatar da ayyukansu ba.
47:5Zai shiryar da su, kuma Ya kyautata hãlãyensu.
47:6Kuma Ya shigarda su Aljanna (wadda) Ya siffanta ta a gare su.
47:7Yã kũ waɗanda suka yi ĩmani! Idan kun taimaki Allah, zai taimake ku, kuma Ya tabbatar da dugãduganku..
47:8Kuma waɗanda suka kãfirta, to, ruɓushi ya tabbata a gare su, kuma (Allah) Ya ɓatar da ayyukansu.
47:9Wannan, sabõda lalle sũ, sun ƙi abin da Allah Ya saukar dõmin haka Ya ɓata ayyukansu.
47:10Shin, ba su yi tafiya ba, a cikin ƙasa, dõmin su gani yadda ãƙibar waɗanda ke a gabãninsu ta kasance? Allah Ya darkãke a kansu. Kuma akwai misãlan wannan ãƙibar ga kãfirai (na kõwane zãmani).
47:11Wancan! Sabõda lalle Allah ne Majiɓincin waɗanda suka yi ĩmãni, kuma lalle, kafirai bãbu wani majiɓinci a gare su.