50:36Kuma da yawa Muka halakar, a gabãninsu, (mutãnen yanzu) ɗaga waɗansu al'ummomi, (waɗanda suke) sũ ne mafi ƙarfin damƙa daga gare su, sa'an nan suka yi bincike a cikin ƙasãshe: 'Kõ akwai wurin tsĩra'? (Babu).
50:37Lalle ne, a cikin wancan, akwai tunãtarwa ga wanda zũciyarsa ta kasance gare shi, kõ kuwa ya jẽfa saurãro, alhãli kuwa yanã halarce (da hankalinsa).
50:38Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun halitta sammai da ƙasã da abin da ke a tsakãninsu, a cikin kwãnaki shida, alhãli wata'yar wahala ba ta shãfe Mu ba.
50:39Sabõda haka, ka yi haƙuri a kan abin da suke fadã, kuma ka yi tasĩhi game da gõdẽ wa Ubangijinka (watau ka yi salla) a gabãnin fitõwar rãnã da gabãnin ɓacẽwarta.
50:40Kuma daga dare, sai ka yi tasbĩhi a gare Shi da bãyan sujada.
50:41Kuma ka saurãra a rãnar da mai kira ke yin kira daga wuri makusanci.
50:42Rãnar da suke saurãron tsãwa da gaskiya. Wancan shĩ ne yinin fita (daga kabari).
50:43Lalle Mũ ne haƙĩƙa, Mu ne ke rãyarwa, kuma Mũ ne ke kashẽwa, kuma zuwa gare Mu kawai ne makõmar take.
50:44Rãnar da ƙasã ke tsattsãgẽwa daga gare su, sunã mãsu gaggãwa. Wancan tãrãwar mutãne ne, mai sauƙi a gare Mu.
50:45Mũ ne mafi sani game da abin da suke faɗi, kuma bã zã ka zama mai tĩlasta su ba. Sabõda haka ka tunatar game da Alƙur'ani, ga wanda ke tsõron ƙyacewaTa.
51:1Inã rantsuwa da iskõki mãsu shẽkar abũbuwa, shẽƙẽwa.
51:2Sa'an nan da girãgizai mãsu ɗaukar nauyi (na ruwa).
51:3Sa'an nan da jirãge mãsu gudãna (a kan ruwa) da sauƙi.
51:4Sa'an nan da Malã'iku mãsu rabon al'amari (bisa umurnin Allah).
51:5Lalle abin da ake yi muku alkawari (da zuwansa), haƙĩƙa gaskiya ne.
51:6Kuma lalle sakamako (ga ayyukanku), haƙĩƙa, mai aukuwa ne