51:52Kamar haka dai wani Manzo bai jẽ wa waɗanda ke gabãninsu ba fãce sun ce: "Mai sihiri ne kõ mahaukaci."
51:53shin, sunã yi wa jũna wasiyya da shi ne? Ã'a, sũ dai mutãne ne mãsu girman kai.
51:54Sai ka jũya daga barinsu, kuma kai ba abin zargi ba ne.
51:55Kuma ka tunãtar, dõmin tunãtarwa tanã amfãnin mũminai.
51:56Kuma Ban halitta aljannu da mutãne ba sai dõmin su bauta Mini.
51:57Bã Ni nufln (sãmun) wani arziki daga gare su, Bã Ni nufin su (yi Mini hidimar) ciyar da Ni.
51:58Lalle Allah, Shĩ ne Mai azurtãwa, Mai ĩkon yi, Mai cikakken ƙarfi.
51:59To, lalle waɗanda suka yi zãlunci sunã da masaki (na ɗĩban zunubi) kamar masakin abõkansu, sabõda haka kada su yi Mini gaggãwa.
51:60Sabõda haka, bone ya tabbata ga waɗanda suka kãfirta, daga rãnar su wadda aka yi musu alkawari.
52:1Inã rantsuwa da ¦ũr (Dũtsen Mũsã).
52:2Da wani littãfi rubũtacce.
52:3A cikin wata takardar fãta shimfiɗaɗɗa.
52:4Da Gidan da aka rãyar da shi (da ibãda).
52:5Da rufin nan da aka ɗaukaka.
52:6Da tẽkun nan da aka cika (da ruwa).
52:7Lalle, azãbar Ubangijinka, haƙĩƙa, mai aukuwa ce.
52:8Bã ta da mai tunkuɗẽwa.
52:9Rãnar da samã ke yin mõtsi tanã kai kãwo.
52:10Kuma duwãtsu nã tafiya sunã shũɗẽwa.
52:11To, bone yã tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa.
52:12Waɗanda suke a cikin kududdufi sunã wãsã.
52:13Rãnar da zã a tunkuɗa su zuwa wutar Jahannama, tunkuɗãwa.
52:14(A ce musu): "Wannan ita ce wutar da kuka kasance kunã ƙaryatãwa game da ita."