54:50Kuma umurninMu bai zamo ba fãce da kalma ɗaya, kamar walƙãwar ido.
54:51Kuma lalle ne haƙĩƙa, Mun halaka irin gayyarku. To, shin, akwai mai tunãni?
54:52Kuma kõwane abu, da suka aikata shi, yanã a cikin littattafai.
54:53Kuma dukkan ƙarami da babba, rubutacce ne.
54:54Lalle mãsu taƙawa sunã a cikin gidãjen Aljanna da kõguna.
54:55A cikin mazaunin gaskiya, wurin Mai ikon yi, Mai iya zartaswa.
55:1(Allah) Mai rahama.
55:2Yã sanar da Alƙur'ani.
55:3Yã halitta mutum.
55:4Yã sanar da shi bayãni (magana).
55:5Rãnã da watã a kan lissãfi suke.
55:6Kuma tsirrai mãsu yãɗo da itãce sunã tawãlu'i.
55:7Kuma samã Ya ɗaukaka ta, Kuma Yã aza sikẽli.
55:8Dõmin kada ku karkatar da sikẽlin.
55:9Kuma ku daidaita awo da ãdalci, kuma kada ku rage sikẽlin.
55:10Kuma ƙasã Yã aza ta dõmin tãlikai.
55:11A cikinta akwai 'ya'yan itãcen marmari da dabĩno mai kwasfa.
55:12Da ƙwãya mai sõshiya da ƙamshi.
55:13To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangjinku kuke ƙaryatãwa?
55:14Yã halitta mutum daga ƙẽkasasshen yumɓu kumar kasko.
55:15Kuma ya halitta aljani daga bira daga wutã.
55:16To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
55:17Ubangjin mafita biyu na rãnã, kuma Ubangijin mafãɗã biyu na rãnã.
55:18To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?