67:27To, lokacin da suka gan ta (azãbar) a kusa, fuskokin waɗanda suka kãfirta suka mũnana, kuma aka ce (musu) wannan shi ne abin da kuka zamo kuna ƙaryatãwa.
67:28Ka ce musu "Idan Allah Ya halaka ni nĩ da wanda ke tãre da ni, ko kuma, Yã yi mana rahama, to, wãne ne zai tserar da kafirai daga wata azãba mai raɗaɗi?"
67:29Ka ce: "Shĩ ne Mai rahama mun yi ĩmãni da Shi, gare Shi muka dogara, saboda haka zã ku san wanda yake a cikin ɓata bayyananniya."
67:30Ka ce: "Ko kun gani, idan ruwanku ya wãyi gari faƙaƙƙe, to, wãne ne zai zo muku da ruwa wani mai ɓuɓɓuga?"
68:1Ñ. Na rantse da alƙalami da abin da (marubũta) suke rubũtãwa.
68:2Kai, sabõda ni'imar Ubangijinka, bã mahaukaci kake ba.
68:3Kuma, lalle, haƙĩƙa kanã da lãdar da bã ta yankewa.
68:4Kuma, lalle haƙiƙa kana a kan hãlãyen kirki, manya.
68:5Don haka, zã ka gani, sũ kuma zã su gani.
68:6Ga wanenku haukã take.
68:7Lalle Ubangijinka Shi ne Mafi sani ga wanda ya ɓace daga tafarkinSa. Kuma Shi ne Mafi sani ga mãsu shiryuwa.
68:8Saboda haka kada ka bi mãsu ƙaryatãwa.
68:9Sunã fatar ka sassauta, su kuma sũ sassauta.
68:10Kada ka bi dukkan mai yawan rantsuwa, walãkantacce.
68:11Mai zunɗe, mai yãwo da gulma.
68:12Mai hana alhẽri mai zãlunci, mai zunubi.
68:13Mai girman kai, bãyan haka kuma la'ĩmi (bã ya son alhẽri).
68:14Sabõda yã kasance mai dũkiya da ɗiya.
68:15Idan ana karanta masa ãyõyinMu, sai ya ce: "Tatsũniyõyin mutãnen farko ne."
68:16Zã Mu yi masa alãma a kan hanci.