70:41Ga Mu musanya waɗanda suke mafi alhẽri, daga gare su. Kuma ba Mu kasance waɗanda ake rinjãya ba.
70:42Sabõda haka ka bar su, su dulmuya, kuma su yi wãsã, har su haɗu da rãnarsu wadda ake yi musu alkawari (da ita).
70:43Rãnar da suke fitowa daga kaburbura da gaugãwa, kamar sũ, zuwa ga wata kafaffiyar (tuta), suke yin gaugãwa.
70:44Maƙaskanta ga idanunsu, wani walakanci yana rufe su. wannan shi ne yinin da suka kasance ana yi musa alkawari (a kansa.)
71:1Lalle ne Mun aiki Nũhu zuwa ga mutãnensa, cẽwa ka yi gargaɗi ga mutãnenka gabãnin wata azãba mai raɗaɗi ta zo musu.
71:2Ya ce: "Ya mutãnena ni, a gare ku, mai gargaɗi ne, mai bayyanãwa."
71:3"Cewa ku bauta wa Allah, ku ji tsõronSa, kuma ku bĩ ni."
71:4"Allah zai gãfarta muku daga zunubanku kuma Ya jinkirta muku zuwa ga ajalin da aka ambata. Lalle ne ajalin Allah idan ya zo, ba za a jinkirta Shi ba, dã kun kasance masana (ga abin da nake faɗã dã, kun bar kãfirci)."
71:5Nũhu) ya ce: "Ya Ubangijina! Lalle ne, na kirãyi mutãnena, a cikin dare da yini."
71:6"To, amma kirana bai ƙãre su ba sai da, gudu (daga gare ni)."
71:7"Kuma lalle ne ni, kõ da yaushe na kirãye su dõmin Ka gãfarta musu, sai su sanya yatsunsu a cikin kunnuwansu, su lulluɓe da tufãfinsu, su dõge ga yin laifi. Sun yi girman kai iyãkar girman kai."
71:8"Sa'an nan lalle ne ni, na kira su, a bayyane."
71:9"Sa'an nan lalle ne, na yi yẽkuwa sabõda su, kuma na gãna da su a cikin asĩri."
71:10"Shi na ce, 'Ku nẽmi gãfara daga Ubangijinku, lalle ne shi Ya kasance Mai gãfara ne."