73:1Yã wanda ya lulluɓe!
73:2Ka tsayu domin yin salla a cikin dare (duka) fãce kaɗan.
73:3Rabinsa, ko ka rage abu kaɗan daga gare shi.
73:4Ko ka ƙara kansa kuma ka kyautata karanta Alƙu'ãni, daki daki.
73:5Lalle ne, Mũ, zã Mu jẽfa maka magana mai nauyi.
73:6Lalle ne, tashin dare shi ne mafi tsananin natsuwa, kuma mafi daidaituwa ga magana.
73:7Lalle ne, kanã da, a cikin yini, wani tasĩhi mai tsawo.
73:8Kuma ka ambaci sũnan Ubangijinka, kuma ka yanke (ƙauna daga kowa ka koma) zuwa gare Shi, yankewa.
73:9Shi ne Ubangijin mafitar rãnã da mafãɗarta, bãbu abin bautawa fãce Shi. Sabõda haka ka riƙe Shi wakili.
73:10Kuma ka yi haƙuri ga abin da suke faɗã, kuma ka ƙaurace musu, ƙauracẽwa mai kyãwo.
73:11Kuma ka bar Ni da mãsu ƙaryatãwa, mawadãta, kuma ka jinkirta musu kaɗan.
73:12Lalle ne, a wurinMu, akwai wasu marũruwa mãsu nauyi da Jahĩm.
73:13Da wani abinci mai mãƙara da azãba mai raɗaɗi.
73:14Rãnar da ƙasa ke raurawa, da duwãtsu kuma duwãtsu su kasance tudun rairayi mai malãlã.
73:15Lalle ne, Mũ. Mun aika zuwa gare ku, wani Manzo mai shaida a kanku, kamar yadda Muka aika wani Manzo zuwaga Fir'auna,
73:16Sai Fir'auna ya saɓa wa Manzon, saboda haka Muka kãma shi kãmu mai tsanani.
73:17To, yãya, idan kun kãfirta, zã ku kãre (azabar) wani yini mai mayar da yãra (tsofaffi) mãsu hurhura.
73:18Sama za ta tsãge a cikinsa, wa'adinsa yã kasance mai aukuwa.
73:19Lalle ne, wannan wata tunãtarwa ce, sai dai wanda ya so, ya kãma hanyar ƙwarai zuwa ga Ubangijinsa.