84:25Fãce waɗanda suka yi ĩmãni, suka aikata ayyukan ƙwarai, sunã da wani sakamako wanda bã ya yankẽwa.
85:1Inã rantsuwa da sama mai taurãrin lissafin shekara.
85:2Da yinin da aka yi alkawarin zuwansa,
85:3Da yini mai shaidu, da yini da ake halarta a cikinsa
85:4An la'ani mutãnen rãmi.
85:5Wato wuta wadda aka hura.
85:6A lõkacin da suke a kan (gefen) ta a zazzaune.
85:7Alhãli sũ, bisa ga abin da suke aikatãwa ga mũminai, sunã halarce.
85:8Kuma ba su tuhumce su ba, fãce kawai domin sun yi ĩmãni da Allah Mabuwãyi, wanda ake gõdewa.
85:9Wanda Yake shi ne da mulkin sammai da ƙasa, kuma Allah a kan kõme halarce Yake.
85:10Lalle ne waɗanda suka fitini mũminai maza da mũminai mãta, sa'an nan ba su tũba ba to, sunã da azãbar Jahannama, kuma sunã da azãbar gõbara.
85:11Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, sunã da gidãjen Aljanna, ƙoramu na gudãna daga ƙarƙashin gidãjen. Wancan abu fa shi ne rabo babba.
85:12Lalle ne damƙar Ubangijinka mai tsanani ce ƙwarai.
85:13Lalle ne Shĩ, Shi ne Mai ƙãga halitta, kuma Ya mayar da ita (bãyan mutuwa).
85:14Kuma Shi ne Mai gãfara, Mai bayyana sõyayya.
85:15Mai Al'arshi mai girma
85:16Mai aikatãwa ga abin da Yake nufi.
85:17Ko lãbãrin rundanõni yã zo maka.
85:18Fir'auna da samũdãwa?
85:19Ã'aha! waɗanda suka kãfirta sunã cikin ƙaryatãwa.
85:20Alhãli, Allah daga bãyansu, Mai kẽwaye su ne (da saninSa).
85:21Ã'aha! Shi Alƙur'ãni ne mai girma.
85:22A cikin Allo tsararre.