86:1Inã rantsuwa da sama da mai aukõwa da dare.
86:2To, mẽ yã sanar da kai abin da ake cẽwa mai aukõwa da dare?
86:3Shi ne taurãron nan mai tsananin haske.
86:4Bãbu wani rai fãce a kansa akwai wani mai tsaro.
86:5To, mutum ya dũba, daga mẽ aka halittã shi?
86:6An halittã shi daga wani ruwa mai tunkuɗar jũna.
86:7Yanã fita daga tsakanin tsatso da karankarman ƙirji.
86:8Lalle ne Shi (Allah), ga mayar da shi (mutum), tabbas Mai iyãwa ne.
86:9Rãnar da ake jarrabawar asirai.
86:10Saboda haka, bã shi da wani ƙarfi, kuma bã shi da wani mai taimako (da zai iya kãre shi daga azãbar Allah).
86:11Ina rantsuwa da sama ma'abũciyar ruwa mai kõmãwa yana yankẽwa.
86:12Da ƙasa ma'abũciyar tsãgẽwa,
86:13Lalle ne shĩ (Alƙur'ãni), haƙĩƙa magana ce daki-daki
86:14Kuma shĩ bã bananci bane
86:15Lalle ne sũ, suna ƙulla kaidi na sõsai.
86:16Kuma Ni, Ina mayar da kaidi (gare su) kamar yadda suke ƙulla kaidi.
86:17Saboda haka, ka yi wa kafirai jinkiri, ka dakata musu, sannu-sannu.
87:1Ka tsarkake sũnan Ubangijinka Mafi ɗaukaka.
87:2Wanda Yã yi halitta sa'an nan Ya daidaita abin halittar.
87:3Kuma Wanda Ya ƙaddara (abin da Ya so) sannan Ya shiryar, (da mutum ga hanyar alhẽri da ta sharri).
87:4Kuma Wanda Ya fitar da makiyãyã.
87:5Sa'an nan Ya mayar da ita ƙeƙasassa, baƙa.
87:6Za mu karantar da kai (Alƙur'ãni) sabõda haka bã zã ka mantã (shi) ba.
87:7Fãce abin da Allah Ya so, lalle ne Shi (Allah) Ya san bayyane da abin da yake bõye.
87:8Kuma za Mu sauƙaƙe maka (al'amari) zuwa ga (Shari'a) mai sauƙi.
87:9Sabõda baka, ka tunãtar, idan tunatarwa zã ta yi amfãni.
87:10Wanda yake tsõron (Allah) Zai tuna.