89:23Kuma a ranar nan aka zo da Jahannama. A ranar nan mutum zai yi tunãni. To, inã fa tunãni yake a gare shi!
89:24Yana dinga cẽwa, "Kaitona, dã na gabatar (da aikin ƙwarai) domin rãyuwata!"
89:25To, a rãnar nan bãbu wani mai yin azãba irin azãbar Allah.
89:26Kuma bãbu wani mai ɗauri irin ɗaurinSa.
89:27Yã kai rai mai natsuwa!
89:28Ka koma zuwa ga Ubangijinka, alhãli kana mai yarda (da abin da Ya ƙaddara maka a dũniya) abar yardarwa (da sakamakon da zã a ba ka a Lãhira).
89:29Sabõbda haka, ka shiga cikin bãyiNa (mãsu bin umurui a dũniya).
89:30Kuma ka shiga AljannaTa (a Lãhira).
90:1Bã sai Na yi rantsuwa da wannan gari ba.
90:2Alhãli kai kanã mai sauka a cikin wannan gari.
90:3Da mahaifi da abin da ya haifa.
90:4Lalle ne, Mun halitta mutum cikin wahala.
90:5Kõ yanã zaton bãbu wani mai iya sãmun iko, a kansa?
90:6Yana cẽwa "Na halakarda dũkiya mai yawa,"
90:7Shin, yana zaton cewa wani bai gan shi ba?
90:8Shin, ba Mu sanya masa idãnu biyu ba?
90:9Da harshe, da leɓɓa biyu.
90:10Kuma ba Mu shiryar da shi ga hanyõyi biyu ba?
90:11To, don mene ne bai shiga Aƙabã ba?
90:12Kuma mene ne ya sanar da kai abin da ake cẽ wa Aƙabã?
90:13Ita ce fansar wuyan bãwa.
90:14Ko kuwa ciyarwa, a cikin yini ma'abũcin yunwa.
90:15Ga marãya ma'abũcin zumunta.
90:16Ko kuwa wani matalauci ma'abũcin turɓãya.
90:17Sa'an nan kuma ya kasance daga waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka yi wa jũna wasiyya da yin haƙuri, kuma suka yi wa jũna wasiyya da tausayi.
90:18Waɗannan ne ma'abũta albarka