94:3Wanda ya nauyayi bãyanka?
94:4Kuma Muka ɗaukaka maka ambatonka?
94:5To, lalle ne tãre da tsananin nan akwai wani sauƙi.
94:6Lalle ne tãre da tsananin nan akwai wani sauƙi.
94:7Sabõda haka idan ka ƙãre (ibãda) sai ka kafu (kana rõƙon Allah).
94:8Kuma zuwa ga Ubangijinka ka yi kwaɗayi.
95:1Inã rantsuwa da Attinu da Azzaitũn.
95:2Da Dũr Sĩnĩna.
95:3Da wannan gari amintacce.
95:4Lalle ne, Mun halitta mutum a cikin mafi kyawon tsayuwa.
95:5Sa'an nan, Muka mayar da shi mafi ƙasƙantar masu rauni
95:6Face waɗanda suka yi imani, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, saboda haka suna da sakamako wanda bã ya yankewa.
95:7To, bãyan haka mẽ ya sanya ka ka ƙaryata sakamako (wanda za a yi a bãyan Tãshin ¡iyãma)?
95:8Ashe Allah bã Shi ne Mafi mãsu hukunci kyãwon hukunci ba?
96:1Ka yi karatu da sunan Ubangijinka, wanda Ya yi halitta.
96:2Ya hahitta mutum daga gudan jini.
96:3Ka yi karatu, kuma UbangiJinka shi ne Mafi karimci.
96:4Wanda Ya sanar (da mutum) game da alƙalami.
96:5Ya sanar da mutum abin da bai sani ba.
96:6A'aha! Lalle, ne mutum haƙĩƙa, yana girman kai (ya ƙi karatu).
96:7Dõmin yã ga kansa, yã wadãta.
96:8Lalle ne zuwa ga Ubangijinka makoma take.
96:9Shin, kã ga wanda ke hana.
96:10Bãwã idan yã yi salla?
96:11Ashe, kã gani, idan (shi bãwan) ya kasance a kan shiriya?
96:12Ko ya yi umurni da taƙawa?