96:13Ashe, kã gani, idan (shi mai hanin) ya ƙaryata, kuma ya jũya bãya?
96:14Ashe, bai sani ba cewa Allah Yanã gani?
96:15A'aha! Lalle ne, idan bai hanu ba, lalle ne zã Mu ja gãshin makwarkwaɗa.
96:16Makwarkwaɗa maƙaryaciya, mai laifi.
96:17Sai ya kirayi ƙungiyarsa.
96:18Zã Mu kirayi zabaniyãwa (mala'iku mãsu girma).
96:19A'aha kada ka bĩ shi. Kuma ka yi tawali'u, kuma ka nemi kusanta (zuwa ga Ubangijinka).
97:1Lalle ne Mũ, Mun saukar da shi (Alƙur'ãni) a cikin Lailatul ƙadari (daren daraja)
97:2To, me ya sanar da kai abin da ake cewa Lailatul ¡adari?
97:3Lailatul ¡adari mafi alheri ne daga wasu watanni dubu.
97:4Mala'iku da Rũhi suna sauka a cikinsa da iznin Ubangijinsu sabõda kowane umurni.
97:5Sallama ne shi daren, har fitar alfijiri.
98:1Waɗanda suka kãfirta daga mũtanen Littafi, da mushirikai, ba su kasance masu gushewa daga gaskiya ba har hujja ta je musu.
98:2Wani Manzo daga Allah, yana karatun wasu takardu masu tsarki.
98:3A cikinsu akwai wasu littafai mãsu ƙĩma da daraja.
98:4Kuma waɗanda aka bai wa Littafi ba su sãɓa wa juna ba face bayan hujjar ta je musu.
98:5Kuma ba a umarce su da kome ba fãce bauta wa Allah suna mãsu tsarkake addinin gare Shi, mãsu karkata zuwa ga addinin gaskiya, kuma su tsai da salla kuma su bãyar da zakka, kuma wannan shi ne addinin waɗanda suke a kan hanyar ƙwarai.