98:6Lalle ne waɗanda suka kafirta daga mutanen Littafi da mushirikai sana cikin wutar Jahannama suna madawwama a cikinta. Waɗannan su ne mafi ashararancin tãlikai.
98:7Lalle ne waɗanda suka yi ĩmani, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, waɗannan su ne mafifita alherin halitta.
98:8Sakamakonsu, a wurin Ubangijinsu, shi ne gidajen Aljannar zama, ƙoramu na gudãna daga ƙarƙashinsu sunã madawwama a cikinta har abada. Allah Ya yarda da su, kuma su, sun yarda da Shi. wannan sakamako ne ga wanda ya ji tsõron Ubangijinsa.
99:1Idan aka girgiza ƙasa, girgizawarta.
99:2Kuma ƙasa ta fitar da kayanta, masu nauyi.
99:3Kuma mutum ya ce "Mẽ neya same ta?"
99:4A rãnar nan, zã ta faɗi lãbãrinta.
99:5cewa Ubangijinka Ya yi umurni zuwa gare ta.
99:6A rãnar nan mutane za su fito dabam-dabam domin a nuna musu ayyukansu.
99:7To, wanda ya aikata (wani aiki) gwargwadon nauyin zarra, na alheri, zai gan shi.
99:8Kuma wanda ya aikata gwargwadon nauyin zarra na sharri, zai gan shi.
100:1Ina rantsuwa da dawãki mãsu gudu suna fitar da kũkan ciki.
100:2Mãsu ƙyasta wuta (da kõfatansu a kan duwatsu) ƙyastawa.
100:3Sa'an nan mãsu yin hari a lokacin asuba.
100:4Sai su motsar da ƙũra game da shi.
100:5Sai su shiga, game da ita (ƙũrar), a tsakãnin jama'ar maƙiya.