100:6Lalle ne mutum mai tsananin butulci ne ga Ubangijinsa.
100:7Lalle ne shi mai shaida ne a kan laifinsa dl haka.
100:8Kuma 1alle ne ga dũkiya shi mai tsananin so ne.
100:9Shin, bã ya da sanin lõkacin da aka tõne abin da yake cikin kaburbura.
100:10Aka bayyana abin da ke cikin zukata.
100:11Lalle ne Ubangijinsu, game da su a ranar nan Mai ƙididdigewa ne?
101:1Mai ƙwanƙwasar (zukata da tsõro)!
101:2Mẽnẽ ne mai ƙwanƙwasa?
101:3Kuma me ya sanar da kai abin da ake ce wa mai ƙwanƙwasa?
101:4Rãnar da mutãne za su kasance kamar 'ya'yan fari mãsu wãtsuwa.
101:5Kuma duwãtsu su kasance kamar gãshin sũfin da aka saɓe.
101:6To, amma wanda ma'aunansa suka yi nauyi.
101:7To, shi yana a cikin wata rayuwa yardadda.
101:8Kuma amma wanda ma'aunansa suka yi sauƙi (bãbu nauyi).
101:9To, uwarsa Hãwiya ce.
101:10Kuma me ya sanar da kai mece ce ita?
101:11Wata wuta ce mai zafi.
102:1Alfahari da yawan dũkiya da dangi ya shagaltar da ku (dagaibada mai amfaninku).
102:2Har kuka ziyarci kaburbura.
102:3A'aha! (Nan gaba) zã ku sani.
102:4Sa'an nan, tabbas, zã ku sani.
102:5Haƙĩƙa, da kuna da sani sani na yaƙĩni.
102:6Lalle ne da kuna ganin Jahĩm.
102:7Sa'an nan lalle ne za ku gan ta, da idanu, bayyane.
102:8Sa'an nan lalle ne za a tambaye ku, a rãnar nan lãbãrin ni'imar (da aka yi muku).