103:1Ina rantsuwa da zãmani.
103:2Lalle ne mutum yana a cikin hasara.
103:3Fãce waɗanda suka yi ĩmani, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, kuma suka yi wa juna wasiyya da bin gaskiya, kuma suka yi wa juna wasiyya da yin haƙuri (su kam, basu cikin hasara).
104:1Bone ya tabbata ga duk mai nune, mai zunɗe (mai raɗa).
104:2Wanda ya tara dũkiya, kuma ya mayar da ita abar tattalinsa.
104:3Yana zaton cẽwa dũkiyarsa za ta dawwamar da shi.
104:4A'aha! Lalle ne zã a jẽfa shi a cikin Huɗama.
104:5Kuma me ya sanar da kai abin da ake ce wa Huɗama?
104:6Wutar Allah ce wadda ake hurawa.
104:7Wadda take lẽƙãwa a kan zukata.
104:8Lalle ne ita abar kullẽwa cea kansu.
104:9A cikin wasu ginshiƙai mĩƙaƙƙu.
105:1Ashe, ba ka ga yadda Ubangijinka Ya aikata ga mutanen giwa ba?
105:2Ashe, bai sanya kaidinsu a cikin ɓata ba?
105:3Kuma Ya sako, a kansu, wasu tsuntsãye, jama'a-jama'a.
105:4Suna jifar su da wasu duwatsu na yumɓun wuta.
105:5Sa'an nan Ya sanya su kamar karmami wanda aka cinye?