Ana lodawa...
106:1Sabõda sãbon ¡uraishawa.
106:2Sãbonsu na tafiyar hunturu da ta bazara.
106:3Sabõda haka sai su bauta wa Ubangijin wannan Gida (Ka'abah).
106:4wanda Ya ciyar da su (Ya hana su) daga yunwa, kuma Ya amintar da su daga wani tsõro.
107:1Shin, ka ga wanda ke ƙaryatãwa game da sakamako?
107:2To, wannan shi ne ke tunkue marãya (daga haƙƙinsa).
107:3Kuma bã ya kwaaitarwa bisa bãyar da abinci ga matalauci.
107:4To, bone yã tabbata ga masallata.
107:5Waɗanda suke masu shagala daga sallarsu.
107:6Waɗanda suke yin riya (ga ayyukansu)
107:7Kuma suna hana taimako.
108:1Lalle ne Mu, Mun yi maka kyauta mai yawa.
108:2Saboda haka, ka yi salla dõmin Ubangijinka, kuma ka sõke (baiko, wato sukar raƙumi).
108:3Lalle mai aibanta ka shi ne mai yankakkiyar albarka.