109:1Ka ce: "Ya kũ kãfirai!"
109:2"Bã zan bautã wa abin da kuke bautã wa ba."
109:3"Kuma kũ, ba ku zama masu bauta wa abin da nake bautã wa ba."
109:4"Kuma nĩ ban zama mai bautã wa abin da kuka bautã wa ba."
109:5"Kuma kũ, ba ku zama mãsu bautã wa abin da nake bautã wa ba."
109:6"Addininku na garẽ ku, kuma addinina yanã gare ni."
110:1Idan taimakon Allah ya zo da cin nasara.
110:2Kuma ka ga mutane suna shiga addinin Allah, ƙungiya-ƙungiya.
110:3To, ka yi tasbihi game da gõde wa Ubangijinka, kuma ka nẽme Shi gafara, lalle Shi (Ubangijinka) Ya kasance Mai karɓar tũba ne.
111:1Hannãye biyu na Abũlahabi sun halaka, kuma ya halaka.
111:2Dũkiyarsa ba ta tsare masa kõme ba, da abin da ya tãra.
111:3Zã ya shiga wuta mai hũruwa.
111:4Tãre da matarsa mai ɗaukar itacen (wuta).
111:5A cikin kyakkyãwan wuyanta akwai igiya ta kaba (Rãnar ¡iyãma).