Ana lodawa...
112:1Ka ce: "Shi ne Allah Makaɗaĩci."
112:2"Allah wanda ake nufin Sa da buƙata."
112:3"Bai haifa ba, kuma ba a haife Shi ba."
112:4"Kuma babu ɗaya da ya kasance tamka a gare Shi."
113:1Ka ce "ina neman tsari ga Ubangijin safiya"
113:2"Daga sharrin abin da Ya halitta."
113:3"Da sharrin dare, idan ya yi duhu."
113:4"Da sharrin mãtã mãsu tõfi a cikin ƙulle-ƙulle."
113:5"Da sharrin mai hãsada idan ya yi hasada."
114:1Ka ce "Ina nẽman tsari ga Ubangijin mutãne."
114:2"Mamallakin mutane."
114:3"Abin bautãwar mutãne."
114:4"Daga sharrin mai sanya wasuwãsi, mai ɓoyewa."
114:5"Wanda ke sanya wasuwãsi a cikin ƙirãzan mutane."
114:6"Daga aljannu da mutane."