Addu'o'i da roƙo a cikin Al-Kur'ani
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَـٰنِ ٱلرَّحِيمِ
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
ٱلْحَمْدُ لِلَّهِ رَبِّ ٱلْعَـٰلَمِينَ
Godiya ta tabbata ga Allah, Ubangijin halittu;
ٱلرَّحْمَـٰنِ ٱلرَّحِيمِ
Mai rahama, Mai jin ƙai;
مَـٰلِكِ يَوْمِ ٱلدِّينِ
Mai nuna Mulkin Rãnar Sakamako.
إِيَّاكَ نَعْبُدُ وَإِيَّاكَ نَسْتَعِينُ
Kai muke bauta wa, kuma Kai muke neman taimakonKa.
ٱهْدِنَا ٱلصِّرَٰطَ ٱلْمُسْتَقِيمَ
Ka shiryar da mu ga hanya madaidaiciya.
صِرَٰطَ ٱلَّذِينَ أَنْعَمْتَ عَلَيْهِمْ غَيْرِ ٱلْمَغْضُوبِ عَلَيْهِمْ وَلَا ٱلضَّآلِّينَ
Hanyar waɗanda Ka yi wa ni'ima, ba waɗanda aka yi wa fushi ba, kuma ba ɓatattu ba.
وَإِذْ يَرْفَعُ إِبْرَٰهِـۧمُ ٱلْقَوَاعِدَ مِنَ ٱلْبَيْتِ وَإِسْمَـٰعِيلُ رَبَّنَا تَقَبَّلْ مِنَّآ ۖ إِنَّكَ أَنتَ ٱلسَّمِيعُ ٱلْعَلِيمُ
Kuma a lõkacin da Ibrãhĩm yake ɗaukaka harsãshin gini ga ¦ãkin, da Ismã'ĩla (suna cẽwa:) "Yã Ubangijnmu! Ka karɓa daga gare mu, lalle ne Kai, Kai ne Mai ji, Mai sani.
رَبَّنَا وَٱجْعَلْنَا مُسْلِمَيْنِ لَكَ وَمِن ذُرِّيَّتِنَآ أُمَّةً مُّسْلِمَةً لَّكَ وَأَرِنَا مَنَاسِكَنَا وَتُبْ عَلَيْنَآ ۖ إِنَّكَ أَنتَ ٱلتَّوَّابُ ٱلرَّحِيمُ
"Ya Ubangijnmu! Ka sanyã mu, mu biyu, waɗanda suka sallama (al'amari) gare Ka, kuma daga zuriyarmu (Ka sanya) al'umma mai sallamãwa zuwa gare Ka, Kuma Ka nũna mana wurãren ibãdar hajjinmu, kuma Ka karɓi tũba a kanmu. Lalle ne Kai, Kai ne Mai karɓar tũba, Mai rahama.
وَإِذَا سَأَلَكَ عِبَادِى عَنِّى فَإِنِّى قَرِيبٌ ۖ أُجِيبُ دَعْوَةَ ٱلدَّاعِ إِذَا دَعَانِ ۖ فَلْيَسْتَجِيبُوا۟ لِى وَلْيُؤْمِنُوا۟ بِى لَعَلَّهُمْ يَرْشُدُونَ
Kuma idan bãyiNa suka tambaye ka daga gare Ni, to, lalle Ni Makusanci ne. Ina karɓa kiran mai kira idan ya kirã Ni. Sabõda haka su nẽmi karɓawaTa, kuma su yi ĩmãni da Ni: tsammãninsu, su shiryu.
Aya 43+ ...