15:1A. L̃.R. Waɗancan ãyoyin littãfi ne da abin karantãwa mai bayyanãwa.
15:2Da yawa waɗanda suka kãfirta suke gũrin dã dai sun kasance Musulmi.
15:3Ka bar su su ci kuma su ji dãdi, kuma gũri ya shagaltar da su, sa'an nan da sannu zã su sani.
15:4Kuma ba Mu halakar da wata alƙarya ba fãce tanã da littafi sananne.
15:5Wata al'umma bã ta gabãtar ajalinta, kuma bã zã su jinkirta ba.
15:6Suka ce: "Yã kai wanda aka saukar da Ambato (Alƙur'ãni) a kansa! Lalle ne kai, haƙĩƙa, mahaukaci ne."
15:7"Dõmin me bã zã ka zo mana da malã'ĩku ba idan ka kasance daga mãsu gaskiya?"
15:8Bã Mu sassaukar da malã'iku fãce da gaskiya, bã zã su kasance, a wannan lõkacin, waɗanda ake yi wa jinkĩri ba.
15:9Lalle Mũ ne, Muka saukar da Ambato (Alƙur'ãni), kuma lal1e Mũ, haƙĩƙa, Mãsu kiyayẽwane gare shi.
15:10Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun aika Manzanni a cikin ƙungiyõyin farko, gabãninka.
15:11Kuma wani Manzo bã ya zuwa gare su fãce sun kasance sunã mãsu, izgili a gare shi.
15:12Kamar wancan ne Muke shigar da shi a cikin zukãtan mãsu laifi.
15:13Bã su yin ĩmãni da shi, kuma haƙĩƙa, hanyar mutãnen farko ta shige.
15:14Kuma dã Mun bũɗe wata ƙõfa daga sama a kansu har suka wuni a ciki sunã tãkãwa.
15:15Lalle ne dã sun ce: "Abin sani kawai, an rufe idãnuwanmu ne. Ã'a, mũ mutãne ne waɗanda aka sihirce."