36:28Kuma ba Mu saukar da waɗansu runduna ba daga sama a kan (halaka) mutãnensa, daga bãyansa, kuma bã zã Mu kasance. Mãsu saukarwa ba.
36:29Ba ta kasance ba face tsawa guda, sa'an nan sai gã su sõmammu.
36:30Yã nadãma a kan bãyĩNa! Wani Manzo bã ya zuwa gare su fãce sun kasance sunã mãsu yi masa izgili.
36:31Ba su gani ba, da yawa Muka halakar da (mutãnen) ƙarnõni a gabãninsu kuma cẽwa su bã zã su kõmo ba?
36:32Kuma lalle bãbu kõwa fãce waɗanda ake halartarwa ne a wurinMu.
36:33Kuma ãyã ce a gare su: ¡asã matacciya, Mu rãyar da ita, Mu fitar da ƙwãya daga gare ta, sai gã shi daga gare ta suke ci.
36:34Kuma Muka sanya, a cikinta (ƙasã), waɗansu gõnaki na dabĩno da inabõbi, kuma Muka ɓuɓɓugar da ruwa daga marẽmari a cikinta.
36:35Dõmin su ci 'ya'yan itãcensa, alhãli kuwa hannãyensu ba su aikata shi ba. Shin, to, bã zã su gõdẽ ba?
36:36Tsarki ya tabbata ga Wanda Ya halitta nau'uka, namiji da mace, dukansu, daga abin da ƙasã ke tsirarwa, kuma daga kansu, kuma daga abin da ba su sani ba.
36:37Kuma ãyã ce a gare su: Dare Muna feɗe rãna daga gare shi, sai gã su sunã mãsu shiga duhu.
36:38Kuma rãnã tanã gudãna zuwa ga wani matabbaci nãta. Wannan ƙaddarãwar Mabuwãyi ne, Masani.
36:39Kuma da watã Mun ƙaddara masa manzilõli, har ya kõma kamar tsumagiyar murlin dabĩno wadda ta tsũfa.
36:40Rãnã bã ya kamãta a gare ta, ta riski watã. Kuma dare bã ya kamãta a gare shi ya zama mai tsẽre wa yini, kuma dukansua cikin sarari guda suke yin iyo.