51:31(Ibrãĩm) ya ce: "To mẽne ne babban al'almarinku, yã kũ Manzanni!"
51:32Suka ce: "Lalle mũ, an aike mu zuwa ga waɗansu mutãne, mãsu laifi.
51:33"Dõmin mu saka musu waɗansu duwãtsu na wani yumɓu (bom).
51:34"Waɗanda aka yi wa alãma daga wajen Ubangijinka, dõmin mãsu ɓarna."
51:35Sa'an, nan Muka fitar da wanda ya kasance a cikinta daga mũminai.
51:36Sai dai ba mu sãmu ba, a cikinta, fãce gida guda na Musulmi.
51:37Kuma Muka bar wata ãyã, a cikinta, ga waɗanda ke jin tsõron azãba, mai raɗaɗi.
51:38Kuma ga Mũsã, a lõkacin da Muka aiko shi zuwa ga Fir'auna da wani dalĩli bayyananne.
51:39Sai ya jũya bãya tãre da ƙarfinsa, kuma ya ce: "Mai sihiri ne kõ kuwa mahaukaci!"
51:40Sabõda haka, Muka kama shi tãre da rundunarsa, sa'an nan Muka jẽfa su a cikin tẽku, alhãli kuwa yanã wanda ake zargi.
51:41Kuma ga Ãdãwa, a lõkacin da Muka aika iska ƙẽƙasasshiya a kansu.
51:42Bã ta barin kõme da ta jẽ a kansa, fãce ta mayar da shi kamar rududdugaggun ƙasũsuwa.
51:43Kuma ga Samũdãwa, a lõkacin da aka ce musu: "Ku ji ɗan dãɗi har wani ɗan lõkaci,"
51:44Sai suka yi girman kai ga umurnin Ubangijinsu, sabõda haka tsãwa ta kãma su, alhãli kuwa sunã kallo.
51:45Ba su kõ sãmu dãmar tsayãwa ba, kuma ba su kasance mãsu nẽman ãgaji ba.
51:46Da mutãnen Nũhu a gabãnin haka, lalle sun kasance waɗansu irin mutãne ne fãsiƙai.
51:47Kuma sama, mun gina ta da wani irin ƙarfi, alhãli kuwa lalle Mũ ne Mãsu yalwatãwa.
51:48Kuma ƙasã Mun shimfiɗa ta, To, madalla da mãsu shimfiɗãwa, Mũ,
51:49Kuma daga kõme Mun halitta nau'i biyu, watakila zã ku yi tunãni.
51:50Sabõda haka ku gudu zuwa ga Allah, lalle nĩ mai gargaɗi kawai ne a gare ku, mai bayyanannen gargaɗi.
51:51Kuma kada ku sanya, tãre da Allah wani abin bautãwa na dabam, lalle nĩ, mai gargaɗi kawai ne a gare ku, mai bayyanannen gargaɗi.