67:1(Allah), Wanda gudãnar da mulki yake ga hannunSa, Ya tsarkaka, kuma Shi Mai ĩko ne a kan kome.
67:2Shi ne Wanda Ya halitta mutuwa da rãyuwa domin Ya jarraba ku, Ya nũna wãye daga cikinku ya fi kyãwon aiki, Shi ne Mabuwãyi, Mai gafara.
67:3Shi ne wanda Ya halitta sammai bakawi, ɗabaƙõƙi a kan jũna, bã za ka ga goggociya ba a cikin halittar (Allah) Mai rahama. Ka sãke dũbawa, ko za ka ga wata ɓaraka?
67:4Sa'an nan ka sake maimaita, dũbãwa, ganinka zai komo maka, gajiyayye, ba da ganin wata naƙasa bã.
67:5Kuma lalle Mun ƙawãta samar farko da fitillu, kuma Muka sanya su abin jifa ga shaiɗanu, kuma Muka yi musu tattalin azãbar Sa'ĩr.
67:6Kuma waɗanda suka kafirce wa Ubangjinsu na da azãbar Jahannama, tã munana ga zamanta makõmarsu.
67:7Idan an jẽfa su a cikinta, sai su ji daga gare ta wata ƙãra, tana tafasa.
67:8Tana kusa ta tsãge domin hushi, ko da yaushe aka jẽfa wani ɓangaren jama'a a cikinta, matsaranta na tambayar su da cewa, "Wani mai gargaɗi bai je muku ba?"
67:9Sai su ce: "I, lalle wani mai gargaɗi ya je mana, sai muka ƙaryata shi, muka ce, 'Allah bai saukar da kome ba, bã ku cikin kõme sai ɓata babba.'"
67:10Kuma suka ce: "Dã mun zamo muna saurãre, kõ muna da hankali, dã ba mu kasance a cikin 'yan sa'ĩr ba."
67:11Wato su yi iƙrãri da laifinsu. Allah Ya la'ani'yan sa'ĩr!
67:12Lalle waɗanda ke tsõron Ubangjinsu, a ɓoye, suna da wata gãfara da wani sakamako mai girma.