3:92Bã zã ku sãmi kyautatãwa ba, sai kun ciyar daga abin da kuke so. Kuma abin da kuka ciyar, kõ mẽne ne, to, lalle ne Allah, gare shi, Masani ne.
3:93Dukan abinci yã kasance halal ne ga Bani lsrã'ĩla, fãce abinda Isrã'ĩla ya haramta wa kansadaga gabãnin saukar da Attaura. Ka ce: "To, ku zo da Attaura sa'an nan ku karantã ta, idan kun kasance mãsu gaskiya ne.
3:94"To, wanda ya ƙirƙira ƙarya ga Allah daga bãyan wannan, to, waɗannan sũ ne azzãlumai."
3:95Ka ce: "Allah Ya yi gaskiya, sabõda haka ku bi aƙĩdar Ibrãhĩma mai karkata zuwa ga gaskiya; kuma bai kasance daga mãsu shirki ba."
3:96Kuma lalle ne, ¦aki na farko da aka aza dõmin mutãne, haƙĩƙa, shi ne wanda ke Bakka mai albarka kuma shiriya ga tãlikai.
3:97A cikinsa akwai ãyõyi bayyanannu; (ga misãli) matsayin Ibrãhĩma. Kuma wanda ya shige shi yã kasance amintacce. Kuma akwai hajjin ¦ãkin dõmin Allah a kan mutãne, ga wanda ya sãmi ĩkon zuwa gare shi, kuma wanda ya kafirta to lalle Allah Mawadãci ne daga barin tãlikai.
3:98Ka ce: "Ya kũ Mutãnen Littãfi! Don me kuke kãfirta da ãyõyin Allah, alhãli kuwa Allah Mai shaida ne a kan abin da kuke aikatãwa?"
3:99Ka ce: "Ya ku Mutãnen Littãfi! Don me kuke taushe wanda ya yi ĩmani, daga hanyar Allah, kuma kunã nẽman ta zama karkatacciya, alhãli kuwa kunã mãsu shaida? Kuma Allah bai gushe daga abin da kuke aikatãwa ba yana Masani."
3:100Ya ku waɗanda suka yi ĩmãni! Idan kun yi ɗã'aga wani ɓangare daga waɗanda aka bai wa Littãfi, zã su mayar da ku kãfirai a bãyan ĩmãninku!