26:1¦. S̃. M̃.
26:2Waɗancan ãyõyin Littãfi ne bayyananne.
26:3Tsammãninka kai mai halakar da ranka ne, dõmin ba su kasance mũminai ba!
26:4Idan Mun so zã Mu saukar, a kansu, da wata ãyã daga sama, sai wuyõyinsu su yini sabõda ita sunã mãsu ƙasƙantar da kai.
26:5Kuma wata tunãtarwa ba ta jẽ musu ba, daga Mai rahama, sãbuwa, fãce sun kasance daga barinta sunã mãsu bijirẽwa.
26:6To, lalle ne, sun ƙaryata, to, lãbãran abin da suka kasance sunã yi na izgili da shi zã ya je musu.
26:7Shin, ba su dũba ba zuwa ga ƙasa, da yawa Muka tsirar a cikinta, daga dukan nau'i mai kyau?
26:8Lalle ne, a cikin wancan akwai ãyã, kuma mafi yawansu ba su kasance mũminai ba.
26:9Kuma lalle ne, Ubangijinka, haƙĩƙa, Shĩ ne Mabuwãyi, Mai rahama.
26:10Kuma a lõkacin da Ubangijinka Ya kirãyi Mũsã, "Ka je wa mutãnen nan azzãlumai.
26:11"Mutãnen Fir'auna bã zã su yi taƙawa ba?"
26:12Ya ce: "Ya Ubangijĩna, nĩ inã tsõron su ƙaryata ni.
26:13"Kuma ƙirjĩna ya yi ƙunci kuma harshẽna bã zai saku ba sabõda haka ka aika zuwa ga Harũna.
26:14"Kuma sunã da wani laifi a kaina, sabõda haka inã tsõron kada su kashe ni."
26:15Ya ce: "Kayya! Ku tafi, kũ biyu, da ÃyõyinMu. Lalle ne, Munã tãre da ku Munã Mãsu saurãre."
26:16"Sai ku je wa Fir'auna, sa'an nan ku ce, Lalle ne, mu, Manzannin Ubangijin halitta ne."
26:17"Ka saki Banĩ Isrã'ila tãre da mu."
26:18Ya ce: "Shin, ba mu yi rẽnonka ba a cikinmu kanã jãrĩri, kuma ka zauna a cikinmu shẽkarudaga lõkacin rãyuwarka?"
26:19"Kuma ka aikata aikinka wanda ka aikata alhãli kai kanã daga butulai?"