37:1Inã rantsuwa da mãsu yin sahu-sahu (a cikin salla kõ yãƙi).
37:2Sa'an nan mãsu yin tsãwa dõmin gargaɗi.
37:3Sa'an nan da mãsu karãtun abin tunãtarwa.
37:4Lalle Abin bautawarku haƙĩƙa ¦aya ne.
37:5Ubangijin sammai da ƙasã da abin da ke tsakãninsu, kuma Ubangijin wurãren fitar rãnã.
37:6Lalle Mũ, Mun ƙãwatãr da sama ta kusa da wata ƙawa, watau taurãri.
37:7Kuma sunã tsari daga dukan Shaiɗan mai tsaurin kai.
37:8Bã zã su iya saurãre zuwa ga jama'a mafi ɗaukaka (Malã'iku) ba, kuma anã jĩfar su daga kõwane gẽfe.
37:9Dõmin tunkuɗẽwa kuma sunã da wata azãba tabbatacciya.
37:10Fãce wanda ya fizgi wata kalma, sai yũla mai haske ta bĩ shi.
37:11Ka tambaye su: "Shin sũ ne mafi wuya ga halittawa, kõ, kuwa waɗanda Muka halitta?" Lalle Mũ, Mun halitta su daga lãkã mai ɗauri.
37:12Ã'a, kã yi mãmãki, alhãli kuwa sunã ta yin izgili.
37:13Kuma idan aka tunãtar da su, bã su tunãwa.
37:14Idan suka ga wata ãyã, sai su dinga yin izgili.
37:15Kuma su ce, "Wannnan bã kõme ba, fãce sihiri, ne bayyananne."
37:16"Shin, idan mun mutu, kuma muka kasance turɓaya da kasũsuwa, ashe, lalle mũ tabbas waɗandaake tãyarwa ne?
37:17"Ashe kõ da ubanninmu na farko?"
37:18Ka ce: "Na'am alhãli kuwa kunã ƙasƙantattu."
37:19Tsãwa guda kawai ce, sai gã su, sunã dũbi.
37:20Kuma su ce: "Yã bonenmu! Wannan ita ce rãnar sakamako."
37:21Wannan ita ce rãnar rarrabẽwa wadda kuka kasance kuna ƙaryatãwa.
37:22Ku tãra waɗanda suka yi zãlunci, da abõkan haɗinsu, da abin da suka kasance sunã bautãwa.
37:23Wanin Allah, sabõda haka ku shiryar da su zuwa ga hanyar Jahĩm.
37:24Kuma ku tsayar da su, lalle su, waɗanda ake yi wa tambaya ne.