53:45Kuma lalle Shĩ ne Ya yi halitta nau'i-nau'i, namiji da mace.
53:46Daga wani ɗigon ruwa guda a lõkacin da ake jẽfa shi a cikin mahaifa.
53:47Kuma a kansa ne ƙãga halitta ta biyu take.
53:48Kuma lalle, Shĩ, Shĩ ne Ya azurta, kuma Ya wadãtar.
53:49Kuma lalle, Shĩ, Shi ne Ubangijin Shi'ira.
53:50Kuma lalle, Shĩ, Shĩ ne Ya halaka Ãdãwa na farko.
53:51Da Samũdãwa, sa'an nan bai rage su ba.
53:52Da mutãnen Nũhu a gabãnin haka, lalle sũ sun kasance mafi zãlunci kuma mafi girman kai.
53:53Da waɗanda aka birkice ƙasarsu, Ya kãyar da su.
53:54Sa'an nan abin da ya rufe su, ya rufe su.
53:55To, da wace daga ni'imõmin Ubangijinka kake yin shakka?
53:56wannan (Muhammadu) mai gargaɗi ne kamar irin mãsu gargaɗi na farko.
53:57Makusanciya fa, tã yi kusa.
53:58Bãbu wani rai, banda Allah, mai iya bãyani gare ta.
53:59Shin, kuma daga wannan lãbãri kuke mãmãki?
53:60Kuma kunã yin dãriya, kuma bã ku yin kũka?
53:61Alhãli kunã mãsu wãsã?
53:62To, ku yi tawãli'u ga Allah, kuma ku bauta (masa).
54:1Sã'a ta yi kusa, kuma wata ya tsãge.
54:2Kuma idan sun ga wata ãyã, sai su juya baya su ce: "Sihiri ne mai dõgẽwa!"
54:3Kuma suka ƙaryata, kuma suka bi son zũciyarsu, alhãli kuwa kõwane al'amari (wanda suke son su tũre daga Annabi) an tabbatar da shi.
54:4Kuma lalle, abin da yake akwai tsãwatarwa a cikinsa na lãbãraiya zo musu.
54:5Hikima cikakka! Sai dai abũbuwan gargaɗi bã su amfãni.
54:6Sabõda haka, ka bar su! Rãnar da mai kiran zai yi kira zuwa ga wani abu abin ƙyama.