55:70A cikinsu, akwai wasu mãtã mãsu kyaun hãlãye, mãsu kyaun halitta.
55:71To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
55:72Mãsu farin idãnu da baƙinsu waɗanda aka tsare a cikin haimõmi.
55:73To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
55:74Wani mutum, gabanin mazajensu bai ɗẽbe budurcinsu ba, kuma haka wani aljani.
55:75To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
55:76Sunã gincire a kan wasu matãsai mãsu kõren launi da katĩfun Abkara kyãwãwa.
55:77To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
55:78Sũnan Ubangjinka, Mai girman Jalãla da Karimci, ya tsarkaka.
56:1Idan mai aukuwa ta auku.
56:2Bãbu wani (rai) mai ƙaryatãwa ga aukuwarta.
56:3(Ita) mai ƙasƙantãwa ce, mai ɗaukakãwa.
56:4Idan aka girgiza ƙasã girgizwa.
56:5Kuma aka niƙe duwãtsu, niƙẽwa.
56:6Sai suka kasance ƙũra da ake wãtsarwa.
56:7Kuma kun kasance nau'i uku.
56:8Watau mazõwa dãma. Mẽne ne mazõwa dãma?
56:9Da mazõwa hagu. Mẽne ne mazõwa hagu?
56:10Da waɗanda suka tsẽre. Sũ wɗanda suka tsẽren nan,
56:11Waɗancan, sũ ne waɗanda aka kusantar.
56:12A ckin Aljannar ni'ima.
56:13Jama'a ne daga mutãnen farko.
56:14Da kaɗan daga mutãnen ƙarshe.
56:15(Sunã) a kan wasu gadãje sãƙaƙƙuu.
56:16Sunã gincire a kansu, sunã mãsu kallon jũna.