56:77Lalle shi (wannan littãfi), haƙĩƙa, abin karantãwa ne mai daraja.
56:78A cikin wani littafi tsararre.
56:79Bãbu mai shãfa shi fãce waɗanda aka tsarkake.
56:80Wanda aka saukar ne daga Ubangijin halitta.
56:81Shin, to, wannan lãbãrin ne kuke mãsu wulãkantãwa?
56:82Kuma kunã sanya arzikinku (game da shi) lalle kũ, ku ƙaryata (shi)?
56:83To, don me idan rai ya kai ga maƙõshi? (Kusa da mutuwa).
56:84Alhãli kuwa kũ, a lõklcin nan, kunã kallo.
56:85Kuma Mũ ne mafi kusanta gare shi daga gare ku, to, amma kũ bã ku gani.
56:86To, don me in dai kun kasance bã waɗanda zã a yi wa sakamako ba?
56:87Ku mayar da shi (cikin jikinsa) har idan kun kasance mãsu gaskiya.
56:88To, amma idan (mai mutuwar) ya kasance daga makusanta,
56:89Sai hũtawa da kyakkyawan abinci da Aljannar ni'ima.
56:90Kuma amma idan ya kasance daga mazõwa dãma,
56:91Sai (a ce masa) aminci ya tabbata a gare ka daga mazõwa dãma.
56:92Kuma amma idan ya kasance daga mãsu ƙaryatãwar, ɓatattun,
56:93Sai wata liyãfa ta ruwan zãfi.
56:94Da ƙõnuwa da Jahĩm,
56:95Lalle wannan, haƙĩƙa, ita ce gaskiya ta yaƙĩni.
56:96Sabõda haka, ka tsarkake sũnan Ubangijinka, Mai karimci.
57:1Abin da ke cikin sammai da ƙasa yã yi tasbĩhi ga Allah. Kuma Shĩ ne Mabuwãyi, Mai hikima.
57:2Shĩ ne da mulkin sammai da ƙasa: Yanã rãyarwa kuma Yanã kashẽwa, kuma Shĩ Mai ikon yi ne a kan kõme.
57:3Shĩ ne Na farko, Na ƙarshe, Bayyananne, Bõyayye, kuma Shĩ Masani ne ga dukkan kõme.