68:43Su fito da idãnu ƙasƙantattu, wulãkanci yana rufe su. Lalle ne a dã sun kasance anã kiran su zuwa, yin sujũdar, alhãli kuwa sunã lãfiya lau, (suka ƙi yi).
68:44Sabõda haka ka bar Ni da mai ƙaryata wanna lãbãri (Alƙur'ãni). Zã Mu yi musu istidrãji daga inda ba su sani ba.
68:45Ina jinkirtã musu, lalle kaidiNa mai ƙarfi ne.
68:46Kõ kana tambayar su wata la'ada ne, sabõda haka sũ, daga wannan tãrar, suke jin an nauyaya musu?
68:47Ko kuma sunã da ilmin gaibu ne, wãto sunã yin rubũtun (abin da suke faɗã daga gare shi) ne?
68:48Sabõda haka, ka yi haƙuri da hukuncin Ubangijinka, kada ka zama kamar Ma'abũcin kĩfi, alõkacin da ya yi kira, alhãli yana cike da hushi.
68:49Ba dõmin ni'ima daga wajen Ubangijinsa tã riske shi ba, lalle ne da an jẽfa shi a cikin wõfintacciyar ƙasa, alhãli yanã abin zargi.
68:50Sai Ubangijinsa Ya zãɓe shi, sa'an nan Ya sanya shi a cikin mutãnen kirki.
68:51Kuma lalle, ne waɗanda suka kãfirta sunã yin kamar su kãyar da kai sabõ da kallonsu (kallon mãmãki), a lokacin da suke jin karãtun Alƙur'ãni, kuma sunã cẽwa, "Lalle ne shi mahaukaci ne!"
68:52Shi (Alƙur'ãni) bai kasance ba, fãce abin tunãtarwa ne ga duka dũniya.
69:1Kiran gaskiya!
69:2Mẽne ne kiran gaskiya?
69:3Kuma mẽ ya sanar da kai abin da ake cẽwa kiran gaskiya?
69:4Samũdãwa da Ãdãwa sun ƙaryatar da kiran gaskiya mai dũkar zũciya!
69:5To, amma Samũdãwa to, an halakãsu da tsãwa mai tsanani.
69:6Kuma amma Ãdãwa to, an halaka su da wata iska mai tsananin sauti wadda ta ƙẽtare haddi.
69:7(Allah) Ya hõre ta a kansu a cikin dare bakwai da yini takwas, biye da jũna, sabõda haka, kana ganin mutãne a cikinta kwance. Kamar sũ ƙirãruwan dabĩno ne, waɗanda suka fãɗi.
69:8To, kõ kanã ganin abin da ya yi saurã daga cikinsu?