69:36"Kuma bãbu wani abinci, sai daga (itãcen) gislĩn."
69:37"Bãbu mai cin sa sai mãsu ganganci."
69:38To, ba sai Nã yi rantsuwa da abin da kuke iya gani ba,
69:39Da abin da bã ku iya gani.
69:40Lalle ne, shi (Alƙur'ani) tabbas maganar wani manzo (Jibirilu) mai daraja ne.
69:41Kuma shi ba maganar wani mawãƙi ba ne. Kaɗan ƙwarai zã ku gaskata.
69:42Kuma bã maganar bõka ba ne. Kaɗan ƙwarai zã ku iya tunãwa.
69:43Abin saukarwã ne daga Ubangijin halitta duka.
69:44Kuma dã (Muhammadu) yã faɗi wata maganã, yã jingina ta garẽ Mu.
69:45Dã Mun kãma shi da dãma.
69:46sa'an nan, lalle ne, dã Mun kãtse masa lakã.
69:47Kuma daga cikinku bãbu wasu mãsu iya kãre (azãbarMu) daga gare shi.
69:48Kuma lalle ne shi (Alƙur'ãni) tanãtarwa ce ga mãsu taƙawa.
69:49Kuma lalle, ne Mũ, wallahi Munã sane da cẽwa daga cikinku alwwai mãsu ƙaryatãwa.
69:50Kuma lalle ne shi (Alƙarãni) wallahi baƙin ciki ne ga kãfirai.
69:51Kuma lalle, ne shi gaskiya ce ta yaƙshẽni.
69:52Sabõda haka, ka tsarkake sũnan Ubangjinka, mai girma.
70:1Wani mai tambaya yã yi tambaya game da azãba, mai aukuwa.
70:2Ga kãfirai, bã ta da mai tunkuɗẽwa.
70:3Daga Allah Mai matãkala.
70:4Malã'iku da Ruhi (Jibrila) sunã tãkãwa zuwa gare Shi, a cikin yini wanda gwargwadonsa, shẽkara dubu hamsin ne.
70:5Sabõda haka, ka yi haƙuri, haƙuri mai kyãwo.
70:6Lalle ne su, sunã ganin ta mai nĩsa.
70:7Kuma Mu, Muna ganin ta a kusa.
70:8Rãnar da sama zã ta kasance kamar narkakkar azurfa.
70:9Kuma duwãtsu su zama kamar saɓin sũfi.
70:10Kuma abõki bã ya tambayar inda wani abõki yake.