73:20Lalle ne, Ubangijinka Yã sani cẽwa, kai kana tsayuwa a kusan kashi biyu daga uku na dare, da rabinsa, da sulusinsa, tãre da wani ɓangare na waɗanda ke tãre da kai. Allah Yake iya ƙaddara dare da yini, Ya san bã zã ku iya lissafa shi ba, sabõda haka Ya karɓi tubarku sai, ku karanta abin da ya sauƙaƙa na Alƙur'ãni. Ya san wasu daga cikinku, zã su yi cĩwo, kuma wasu zã su yi tafiya cikin ƙasa suna nẽman falalar Allah da fatauci, kuma wasu zã su yi yãƙi a cikin banyar Allah. Sabõda haka ku karanta abin da ya sauƙaƙa daga gare shi, kuma ku tsai da salla kuma ku bãyar da zakka, kumaa ku bai wa Allah rance, rance mai kyãwo. Kuma abin da kuka gabatar dõmin kanku, na alhẽri, zã ku sãme shi a wurin Allah zai kasance mafifici (daga wanda kuka ajiye) kuma zai fi girma ga sakamako, kuma ku rõƙi Allah gãfara; lalle ne Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.
74:1Yã wanda ya lulluɓa da mayãfi.
74:2Ka tãshi dõmin ka yi gargaɗi
74:3Kuma Ubangijinka, sai ka girmama Shi,
74:4Kuma tutãfinka, sai ka tsarkake su,
74:5Kuma gumãka, sai ka ƙaurace musu.
74:6Kada ka yi kyauta kana nẽman ƙãri
74:7Kuma sabõda Ubangijinka? Sai ka yi haƙure
74:8To, idan aka yi bũsa a cikin ƙaho.
74:9To, wannan, a rãnar nan, yini ne mai wuya
74:10A kan kãfirai, bã mai sauƙi ba ne.
74:11Ka bar Ni da wanda Na halitta, yana shi kaɗai,
74:12Kuma Na sanya masa dũkiya shimfiɗaɗɗiya
74:13Da ɗiyã halartattu,
74:14Kuma Na shimfiɗa? masa kõme shimfiɗãwa.
74:15Sa'an nan, yanã kwaɗayin in yi masa ƙãri!
74:16Faufau! Lalle ne, shĩ yã kasance, ga ãyõyinMu, mai tsaurin kai.
74:17Zã Ni kallafa masa wahala mai hauhawa.
74:18Lalle ne, Shi, yã yi tunãni, kuma yã ƙaddara (abin da zai faɗã game da Alƙur'ãni)