75:20A'aha! Bã haka ba kunã son mai gaugawar nan (duniya) ne.
75:21Kunã barin ta ƙarshen (Lãhira).
75:22Wasu huskõki, a rãnar nan, mãsu annuri ne.
75:23Zuwa ga Ubangijinsu mãsu kallo ne.
75:24Wasu huskõki, a rãnar nan, mãsu gintsẽwa ne.
75:25Sunã zaton a sako musu masĩfa mai karya tsatso.
75:26A'aha! Iadan (rai) ya kai ga karankarmai.
75:27kuma aka ce: "Wãne ne mai tawada?"
75:28Kuma ya tabbata cẽwa rabuwa dai ce.
75:29Kuma ƙwabri ya lauye da wani ƙwabri.
75:30Zuwa ga Ubangijinka, a rãnar nan, magargaɗa take.
75:31To, bai gaskatã ba, kuma bai yi salla ba!
75:32Amma dai ya ƙaryata, kuma ya jũya baya!
75:33Sa'an nan, ya tafi zuwa ga mutãnensa, yana tãƙama.
75:34Halaka tã tabbata a gare ka, sa'an nan ita ce mafi dãcewa.
75:35Sa'an nan, wata halaka tã tabbata a gare ka dõmin tã fi dãce wa.
75:36Shin, mutum nã zaton a bar shi sagaga (wãto bãbu nufin kõme game da shi)?
75:37Bai kasance iɗgo na maniyyi ba, wanda ake jefarwa (a cikin mahaifa)
75:38Sa'an nan, ya zama gudan jini, sa'an nan Allah Ya halitta shi, sa'an nan Ya daidaita gaɓõɓinsa;
75:39Sa'an nan, Ya sanya daga gare shi, nau'i biyu: namiji damace?
75:40Ashẽ wannan bai zama Mai iko ba bisa ga rãyar da matattu?
76:1Lalle ne, wata mudda ta zamani tã zo a kan mutum, bai kasance kõme ba wanda ake ambata.
76:2Lalle ne, Mũ Mun halitta mutum daga ɗigon ruwa garwayayye, Muna jarraba shi, sabõda haka Muka sanya shi mai ji mai gani,
76:3Lalle ne, Mũ, Mun shiryar da shi ga hanyar ƙwarai, ko ya zama mai gõdiya, kuma ko ya zama mai kãfirci.
76:4Lalle ne, Mũ, Mun yi tattali, dõmin kãfirai, sarƙoƙi da ƙuƙumma da sa'ĩr.
76:5Lalle ne, mutãnen kirki zã su sha daga finjãlin giya abin gaurayarta yã kãsance kãfur ne.