76:26Daga dare, sai ka yi sujũda gare Shi, kuma ka tsarkake Shi darẽ mai tsawo.
76:27Lalle ne, waɗannan suna son mai gaugãwa (dũniya) kuma suna bari, a bãyansu, wani yini mai nauyi.
76:28Mũ ne Muka halitta su kuma Muka, ƙarfafa halittarsu, kuma idan Mun so, za Mu musanyâ su da wasu mutane kwatankwacinsu, musanyawa.
76:29Lalle ne, wannan wata tunãtarwa ce, saboda wanda ya so ya riƙa hanyar kirki zuwa ga Ubangijinsa.
76:30Kuma, bã zã ku so ba, sai Allah Ya so, lalle ne Allah Yã kasance Masani' Mai hikima.
76:31Yana shigar da wanda Ya so a cikin rahamarsa, kuma azzãlumai, Yã yi musu tattalin wata azãba mai raɗaɗi.
77:1Ina rantsuwa da iskõkin da ake sakõwa jẽre, sunã bin jũna.
77:2Sa'an nan, su zamã iskõki mãsu ƙarfi suna kaɗãwa da ƙarfi.
77:3Kuma, mãsu watsa rahama wãtsãwa.
77:4sa'an nan, da ãyõyi mãsu rarrabe gaskiya da ƙarya rarrabẽwa.
77:5Sa'an nan da malã'iku mãsu jẽfa tunãtarwa ga Manzanni.
77:6Domin yanke hamzari ko dõmin gargadi.
77:7Lalle ne, abin da ake yi muku wa'adi da shi tabbas mai aukuwa ne
77:8To, idan taurãri aka shãfe haskensu.
77:9Kuma, idan sama aka tsãge ta.
77:10Kuma, idan duwãtsu aka nike su.
77:11Kuma, idan manzanni aka ƙayyade lõkacin tãra su.
77:12Domin babbar rãnar da aka yi wa ajali.
77:13Domin rãnar rarrabẽwa.
77:14Kuma, me ya sanar da kai rãnar rarrabẽwa?
77:15Bone yã tabbata a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
77:16Ashe, ba Mu halakar da (mãsu ƙaryatãw) na farko ba.
77:17Sa'an nan, kuma zã Mu biyar musu da na ƙarshe?
77:18Haka nan, Muke aikatãwa da mãsu yin laifi.
77:19Bone yã tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa!