80:1Yã game huska kuma ya jũya bãya.
80:2Sabõda makãho yã je masa.
80:3To, me ya sanar da kai cẽwa watakila shi ne zai tsarkaka.
80:4Ko ya tuna, dõmin tunãwar ta amfane shi?
80:5Amma wanda ya wadãtu da dũkiya.
80:6Sa'an nan kai kuma ka ɗora bijira zuwa gare shi!
80:7To, me zai cũce ka idan bai tsarkaka ba?
80:8Kuma, amma wanda ya zomaka yana gaugãwa.
80:9Alhãli shĩ yanã jin tsõrõn Allah.
80:10Kai kuma kã shagala ga barinsa!
80:11A'aha! Lalle ne, wannan tunãtarwa ce.
80:12Sabõda wanda ya so ya tunaShi (Allah).
80:13(Tunãtarwa ce) ta cikin littafai abãban girmamãwa,
80:14Abãban ɗaukakãwa, abãban tsarkakẽwa.
80:15A cikin hannãyen mala'iku marubũta.
80:16Mãsu daraja, mãsu ɗã'a ga Allah.
80:17An la'ani mutum (kafiri). Mẽ yã yi kãfircinsa!
80:18Daga wane abu, (Allah) Ya halitta shi?
80:19Daga ɗigon maniyyi, Ya halitta shi sa'an nan Ya ƙaddarã shi (ga halaye).
80:20Sa'an nan, hanyarsa ta fita Ya sauƙaƙe masa.
80:21Sa'an nan, Ya matar da shi sai Ya sanya shi a cikin kabari.
80:22Sa'an nan, idan Ya so lalle ne zai tãyar da shi.
80:23Haƙĩƙa bai i da aikata abin da Allah Ya umurce shi ba (lõkacin sanya shi a cikin kabari).
80:24To, mutum ya dũba zuwa ga abincinsa.
80:25Lalle ne Mũ, Mun zuo ruwa, zubõwa.
80:26Sa'an nan, Muka tsattsãge ƙasa tsattsagewa.
80:27Sa'an nan, Muka tsirar da ƙwaya, a cikinta.
80:28Da inabi da ciyãwa.
80:29Da zaitũni da itãcen dabĩno.
80:30Da lambuna, mãsu yawan itãce.
80:31Da 'yã'yan itãcen marmari, da makiyãyã ta dabbõbi.
80:32Domin jin dãɗi a gare ku, ku da dabbobinku.
80:33To, idan mai tsãwa (busa ta biyu) ta zo.
80:34Rãnar da mutum yake gudu daga ɗan'uwansa.
80:35Da uwarsa da ubansa.
80:36Da mãtarsa da ɗiyansa.
80:37Ga kõwane mutum daga cikinsu, a rãnar nan akwai wani sha'ani da ya ishe shi.
80:38Wasu huskõki, a rãnar nan, mãsu haske ne.
80:39Mãsu dãriya ne, mãsu bushãra.
80:40Wasu huskõki, a rãnar nan, akwai ƙũra a kansu.