82:1Idan sama ta tsãge.
82:2Kuma idan taurãri suka wãtse.
82:3Kuma idan tẽkuna aka facce su.
82:4Kuma idan kaburbura aka tõne su.
82:5Rai yã san abin da ya gabatar, da abin da yã jinkirtar.
82:6Yã kai mutum! Mẽ ya rũɗe ka game da Ubangijinka, Mai karimci.
82:7Wanda Ya halitta ka sa'an nan ya daidaitã ka, Ya kuma tsakaitã ka.
82:8A cikin kõwace irin sũra Ya so Ya ginã ka a kanta.
82:9A'aha, bã haka ba, kuna ƙaryatãwa game da sakamako!
82:10Lalle ne, a kanku, haƙiƙa akwai matsara.
82:11Mãsu daraja, marubũta.
82:12Sunã sanin abin da kuke aikatãwa.
82:13Lalle ne, mãsu ɗã'ã ga Allah, dãhir, suna cikin ni'ima.
82:14Kuma lalle ne, fãjirai, dãhir, sunã cikin Jahĩm.
82:15Zã su shigẽ ta a rãnar sakamako.
82:16Bã zã su faku daga gare ta ba.
82:17Kuma mẽ ya sanar da kai abin da ake cẽ wa rẽnar sakamako?
82:18Sa'an nan, mẽ ya sanar da kai abin da ake cẽ wa rãnar sakamako?
82:19Rãnã ce da wani rai ba ya iya mallakar kõme dõmin wani rai al'amari, a rãnar nan, ga Allah (ɗai) yake.
83:1Bone ya tabbata ga mãsu naƙƙasãwa.
83:2Waɗanda suke idan suka auna daga mutãne suna cika mũdu.
83:3Kuma idan sun auna musu da zakka ko da sikẽli, suna ragẽwa
83:4Ashe! Waɗancan bã su tabbata cẽwa lalle sũ, ana tãyar da su ba?