83:34To, yau fa (a Lãhira] waɗanda suka yi ĩmãni, sũ ke yi wa kãfirai dãriya.
83:35A kan karagu, suna ta kallo.
83:36Shin an sãka ma kãfirai abin da suka kasance suna aikatawa?
84:1Idan sama ta kẽce,
84:2Ta saurari Ubangijinta, kuma aka wajabta mata yin saurãron,
84:3Kuma idan ƙasã aka mĩƙe ta,
84:4Kuma ta jẽfar da abin da yake a cikinta, tã wõfinta daga kõme.
84:5Kuma ta saurãri Ubangijinta, aka wajabta mata yin saurãren,
84:6Ya kai mutum! Lalle ne kai mai aikin wahal da kai ne zuwa ga Ubangijinka, wahala mai tsanani, To, kai mai haɗuwa da Shi ne.
84:7To, amma wanda aka bai wa littãfinsa da damansa.
84:8To, za a yi masa hisãbi, hisãbi mai sauƙi.
84:9Kuma ya jũya zuwa ga iyãlinsa (a cikin Aljanna), yanã mai raha.
84:10Kuma amma wanda aka bai wa littãfinsa, daga wajen bãyansa.
84:11To, zã shi dinga kiran halaka!
84:12Kuma ya shiga sa'ĩr.
84:13Lal1e ne shi, yã kasance (a dũniya) cikin iyãlinsa yanã mai raha.
84:14Lalle ne yã yi zaton bã zai kõmo ba.
84:15Na'am! Lalle ne, Ubangijinsa Ya kasance Mai gani gare shi.
84:16To, ba sai Nã rantse da shafaƙi ba.
84:17Da dare, da abin da ya ƙunsa.
84:18Da watã idan (haskensa) ya cika.
84:19Lalle ne kunã hawan wani hãli daga wani hãli.
84:20To, mẽ ya sãme su, ba su yin ĩmãni?
84:21Kuma idan an karanta Alkur'ãni a kansu, bã su yin tawãli'u?
84:22Ba haka ba! waɗanda suka kãfirta, sai ƙaryatãwa suke yi.
84:23Alhãli Allah Shĩ ne Mafi sani ga abin a suke tãrãwa.
84:24Saboda haka, ka yi musu bushãra da azãba mai raɗaɗi.