87:11Kuma shaƙiyyi, zai nisanceta,
87:12Wanda zai shiga wutar da tã fi girma.
87:13Sa'an nan bã zai mutu ba a cikinta, kuma bã zai rãyu ba.
87:14Lalle ne wanda ya tsarkaka (da ĩmãni) yã sãmu babban rabo.
87:15Kuma ya ambaci sũnan Ubangijinsa, sa'an nan yã yi salla.
87:16Ba haka ba! Kunã zãɓin rãyuwa ta kusa dũniya.
87:17Alhãli Lãhira ita ce mafi alheri kuma mafi wanzuwa.
87:18Lalle ne, wannan yanã a cikin littafan farko.
87:19Littaffan Ibrãhĩm da Mũsã.
88:1Lalle ne labãrin (¡iyãma) mai rufe mutãne da tsoronta yã zo maka?
88:2Wasu huskõki a rãnar nan ƙasƙantattu ne.
88:3Mãsu aikin wahala ne, mãsu gajiya.
88:4Zã su shiga wata wuta mai zãfi.
88:5Ana shãyar da su daga wani marmaro mai zãfin ruwa.
88:6Ba su da wani abinci fãce dai daga danyi.
88:7Bã ya sanya ƙiba, kuma bã zai wadãtar daga yunwa ba.
88:8Wasu huskõki a rãnar nan mãsu ni'ima ne.
88:9Game da aikinsu, masu yarda ne.
88:10(Suna) a cikin Aljanna maɗaukakiya.
88:11Bã zã su ji yãsassar magana ba, a cikinta.
88:12A cikinta akwai marmaro mai gudãna.
88:13A cikinta akwai gadãje maɗaukaka.
88:14Da kõfuna ar'aje.
88:15Da filõli jẽre,
88:16Da katifu shimfiɗe.
88:17Ashe to bã zã su dũbãwa ba ga rãƙumã yadda aka halitta su?
88:18Da zuwa ga sama yadda aka ɗaukaka ta?
88:19Da zuwa ga duwãtsu yadda aka kafa su?
88:20Da zuwa ga ƙasa yadda aka shimfiɗã ta?
88:21sabõda haka, ka yi wa'azi, kai mai yin wa'azi ne kawai.
88:22Ba ka zama mai ĩkon tanƙwasãwa a kansu ba.