88:23Fãce dai duk wanda ya jũya bãya, kuma ya kãfirta.
88:24To, Allah zai yi masa azãba, azãbar nan da take mafi girma.
88:25Lalle ne, zuwa gare Mu kõmõwarsu take.
88:26Sa'an nan lalle ne aikinMu ne Mu yi musu hisãbi.
89:1Inã rantsuwa da alfijiri.
89:2Da darũruwa gõma.
89:3Da (adadi na) cikã da (na) mãrã.
89:4Da dare idan yana shũɗewa.
89:5Ko a cikin waɗannan akwai abin rantsuwa ga mai hankali (da yake kange shi daga zunubi)?
89:6Ba ka ga yadda Ubangijinka Ya aikata da Ãdãwa ba?
89:7Iramawa mãsu sakon ƙĩrar jiki.
89:8Waɗanda ba a halitta kwatankwacinsu ba a cikin garũruwa (na dũniya).
89:9Da samũdãwa waɗanda suka fasa duwãtsu a cikin Wadi suka yi gidãje)?
89:10Da Fir'auna mai turãku.
89:11Waɗanda suka ƙẽtare iyãkarsu, a cikin garũruwa?
89:12Sabõda haka, suka yawaita yin ɓarna a cikinsu.
89:13Sabõda haka Ubangijinka Ya zuba musu bũlãlar azãba.
89:14Lalle ne, Ubangijinka Yana nan a mafaka.
89:15To, amma fa mutum idan Ubangijibsa Ya jarraba shi, wãto Yã girmama shi kuma Ya yi masa ni'ima, sai ya ce: "Ubangijina Ya girmama ni."
89:16Kuma idan Ya jarraba shi, wãto Ya ƙuntata masa abincinsa, sai ya ce: "Ubangijina Ya walãkanta ni."
89:17A'aha! Bari wannan, ai bã ku girmama marãya!
89:18Bã ku kwaɗaitã wa jũnanku ga (tattalin) abincin matalauci!
89:19Kuma kuna cin dũkiyar gãdo, ci na tãrãwa.
89:20Kuma kuna son dũkiya, so mai yawa.
89:21A'aha! Idan aka niƙa ƙasa niƙewa sosai.
89:22Kuma Ubangijinka Ya zo, alhãli malã'iku na jẽre, safũ- safu.