90:19Kuma waɗanda suka kãfirta da ãyõyinMu, sũ ne ma'abũta shu'umci
90:20A kansu akwai wata wuta abar kullewa.
91:1Ina rantsuwa da rãnã da hantsinta.
91:2Kuma da wata idan ya bi ta.
91:3Da yini a lõkacin da ya bayyana ta.
91:4Da dare a lõkacin da ya ke rufe ta.
91:5Da sama da abin da ya gina ta.
91:6Da ƙasã da abin da ya shimfiɗa ta.
91:7Da rai da abin da ya daidaita shi.
91:8Sa'an nan ya sanar da shi fãjircinsa da shiryuwarsa.
91:9Lalle ne wanda ya tsarkake shi (rai) ya sãmi babban rabo.
91:10Kuma lalle ne wanda ya turbuɗe shi (da laifi) ya tãɓe.
91:11Samũdãwa sun ƙaryata (Annabinsu), dõmin girman kansu.
91:12A lõkacin da mafi shaƙãwarsu ya tafi (wurin sõke rãkumar sãlihu).
91:13Sai Manzon Allah ya gaya musu cewa: "Ina tsõratar da ku ga rãƙumar Allah da ruwan shanta!"
91:14Sai suka ƙaryata shi, sa'an nan suka sõke ta. Sabõda haka Ubangijinsu Ya darkãke su, sabõda zunubinsu. Sa'an nan Ya daidaita ta (azãbar ga mai laifi da maras laifi).
91:15Kuma bã ya tsõron ãƙibarta (ita halakãwar).
92:1Inã rantsuwa da dare a lõkacin da yake rufẽwa.
92:2Da yini a lõkacin da yake kuranyẽwa.
92:3Da abin da ya halitta namiji da mace.
92:4Lãlle ne ayyukanku, dabam-dabam suke.
92:5To, amma wanda ya yi kyauta, kuma ya yi taƙawa.
92:6Kuma ya gaskata kalma mai kyãwo.
92:7To, zã Mu sauƙaƙe masa har ya kai ga sauƙi.
92:8Kuma amma wanda ya yi rõwa, kuma ya wadãtu da kansa.
92:9Kuma ya ƙaryatar da kalma mai kyãwo.